Kungiyoyin Agaji da Hisbah a Karamar Hukumar Mani Sun Baiwa Hukumar Hisbah Ta Katsina Goyon Baya
- Katsina City News
- 26 Sep, 2024
- 220
A ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, gamayyar kungiyoyin agaji da Hisbah na Ƙaramar Hukumar Mani sun kai ziyarar jaddada goyon baya ga Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, karkashin jagorancin Babban Kwamanda, Sheikh Dakta Abu Ammar.
Ziyarar, wadda Malam Hambali Lawal Mani ya jagoranta, ta fito da nasarorin hadin gwiwar da ake yi tsakanin kungiyoyin agaji da Hukumar Hisbah, tare da jinjina wa shugabancin Dakta Abu Ammar bisa kokarinsa na tabbatar da kyawawan manufofi a jihar.
Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Katsina, Dakta Aminu Usman (Abu Ammar), ya bayyana farin cikinsa kan wannan ziyara, yana mai kira da a kara hada kai wajen cigaba da yaki da duk wani abin da ya saba wa al’ada da tarbiyya a Karamar Hukumar Mani da ma jihar baki ɗaya.
Sannan, Dakta Aminu Usman ya bayar da shawarwari kan yadda za a kara inganta hadin kai tsakanin Hisbah da kungiyoyin agaji domin cimma nasarorin da za su amfani al’umma wajen kare mutunci da tarbiyya.