Cika shekaru 37 da ƙirƙiro Jihar Katsina: Sheikh Pantami zai gabatar da wa’azi
- Katsina City News
- 22 Sep, 2024
- 229
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Daga cikin bukukuwan cika shekara 37 da ƙirƙiro Jihar Katsina, ana sa ran tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami zai gabatar da wa’azi a Katsina mai taken ‘Riƙon Amana’.
Manufar zaɓo taken wa’azin shi ne a tunatar da masu madafun iko a jihar su san mahimmancin riƙon amana da nauyin da Allah ya ɗora masu wajen jagoranci.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Dakta Salisu Bala Zango ya sanar da haka da ya ke hira da manema labarai akan irin shirye-shiryen da aka tsara a ranakun bukukuwan.
Ya ce, akwai taro na musamman wanda duk masu ruwa da tsaki a jihar za su halarta inda za a duba baya, a ga inda aka tsaya da kuma inda aka dosa.
Haka kuma, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar za ta ƙarrama tsoffin jami’an gwamnati da waɗanda ke aiki da suka nuna ƙwazo.
Dakta Bala ya kara da cewa, a shekarun baya jihar Katsina ta samu cigaba ta fannin ilimi, kiyon lafiya, harkokin noma da bunƙasa ƙasa.
Ya kuma ce, gwamnatocin da suka wuce sun yi iya nasu ƙoƙarin wajen ciyar da jihar gaba ga kuma yanzu gwamna Dikko Raɗɗa da ke nasa ƙoƙarin wajen samar da ababen more rayuwa.
Haka kuma ya ƙara da cewa, gwamnatin Dikko Raɗɗa ta taka rawar gani wajen samar da dauwamammen zaman lafiya a jihar da ƴan ta’adda suka kusa lalatawa.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su taya gwamna Dikko Raɗɗa murnar cika shekaru 37 da ƙirƙiro jihar.
Har’ilayau, cikin bukukuwan, kungiyar ƴan jaridu reshen jihar Katsina, ta shirya gudanar da taron tunawa da ɗan gwagwarmaya kuma Malamin Tarihi a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, marigayi Dakta Yusuf Bala Usman.