'Yansanda A Katsina Sun Tarwatsa Wasu Gungun 'Yan Fashi Tare Da Kwato Kayan Sata Na Naira Miliyan Hudu
- Katsina City News
- 20 Sep, 2024
- 378
Katsina Times
A cikin wani gagarumin samame, rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama gungun ƴan fashi su bakwai da ake zargi da aikata manyan laifuka, inda ta kwato kayan sata da kimarsu ta kai naira miliyan huɗu.
ASP Abubakar Sadiq Aliyu, mai magana da yawun rundunar, ya bayyana cewa an yi nasarar kama su ne a ranar 8 ga Satumba, 2024 da misalin karfe 2:00 na safe, bayan an gudanar da bincike mai zurfi daga ofishin yan sanda na yankin Funtua.
Ana zargin waɗanda aka kama da kwace wa wani direba kayansa da suka haɗa da atamfofi da kayan ɗinki, bayan sun toshe hanyar Kano-Zariya da duwatsu, suka tilasta wa direban tsayawa, suka ɗaure shi suka kwace masa kayan.
Kayan da aka kwato sun haɗa da:
- Ɗunkulallun atamfofi da kayan las guda 94
- Ɗunkulallun wasu kayan guda biyu
- Motocin aiki guda biyu (Volkswagen Golf III da Ford Focus)
Bincike ya nuna waɗanda ake zargin sun yi amfani da waɗannan motocin wajen sace kayan masarufi irin su hatsi da mai dafa abinci.
Haka zalika rundunar ta kara kama wasu mutane uku da bindigar gida
- An kama Bala Muhammad, wanda ya shahara wajen satar babura, an kuma kwato motar sata
- An kama mutane biyu da ake zargi da sace-sace da lalata kayayyaki; an kwato kayayyakin
- Aliyu Masa’udu, ɗan shekara 18, wanda ya shahara wajen satar babura, an kama shi ya amsa laifin aikata wasu sace-sacen
- An kama Hussaini Idris, ɗan shekara 37, da ake zargi da satar manyan Farantan Sola masu amfani da hasken rana guda uku mai karfin 400 KVA
"Rundunar ta ƙuduri aniyar ci gaba da yaki da laifuka don tabbatar da tsaro a cikin al'umma," in ji ASP Aliyu.