Yan Majalisar Wakilai Sun Bukatar Kasar Canada Ta Binciki Matar Nan Mai Barazanar Kashe al'ummar Yarbawan Nijeriya
- Katsina City News
- 30 Aug, 2024
- 421
Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi Jakadan Kasar Canada ya sa gwamnatin kasarsa ta yi bincike mai zurfi domin hukunta wata mata 'yar Najeriya mazauniyar garin Ontario mai suna Amaka Patience Sunnberger kan furucin da ta yi na nuna kiyayya a dandalin sada zumunta na TikTok
Ita dai Amaka ta fito ne karara da alwashin za ta zuba guba cikin abincin da ‘yan kabilar Yarbawa da ‘Yan Jihar Edo da suke aiki tare a Canada za su ci . Sai dai wasu ‘yan kasa na ganin ba za a girmama maganan ‘yan majalisa ba wasu kuma na ganin da walakin goro a miya.
Amaka da ‘yan uwanta suna tattaunawa ne kan dandalin tiktok lokacin da ta yi barazanar cewa za ta sa guba a abinci da ruwan da mutanen za su sha, sai su mutu. Amaka ta ce za ta ci gaba da yin haka har sai duk sun mutu saboda a cewar ta wasu kabilun sun mayar da kabilar Igbo saniyar ware kuma lokaci ya yi da za a kawar da su.
Amaka ta yi barazanar fara sanya wa abokan aikinta Yarbawa guba a wurin aiki idan ta koma bakin aiki washe gari.
To sai dai wannan batu ya ba tsohon Jakadan Najeriya a Kasar Sudan, Suleiman Dahiru mamaki inda ya ce ya yi jakadanci a kasashe 9 a rayuwar sa bai taba ganin irin haka ba. Dahiru ya ce wadannan kalamai sun nuna irin rarrabuwar kawuna ne da ke faruwa a kasar Najeriya, inda ya yi kira da a kula a duba dokoki na kasa da kasa domin a yi wa tukka hanci wajen hukunta wannan mata.
Shi ma kwararre a fanin zamantakewan dan adam, Abubakar Aliyu Umar ya yi tsokaci kan matakin da majalisar wakilai ta dauka ne. Inda ya ce babu wanda zai dauki kira da Majalisar wakilai ta yi da muhummanci domin ba a girmama su a kasashen waje.
Abubakar ya ce wannan kira na Majalisa ba zai yi tasiri ba saboda an riga an zubar da mutuncin Najeriya a kasashen waje. Gara a bari kasar da ta ke su dauki mataki akan ta idan sun gadama amma ba wai saboda ‘yan majalisa sun sa baki ba.
Shi ma Malam Aminu Jumare ya baiyana ra'ayin da ya goyi bayan a dauki mataki a kanta a kasar da ta ke yana mai cewa Kasar Canada ta yi bincike mai zurfi domin akwai alamun wata kullalliya a tsakanin ta da abokan aikin ta. Aminu ya ce kowace kasa tana da dokoki, saboda haka yana ganin babu wani dalilin kawo ta gida Najeriya. Kasar Canada ta dauki mataki a kanta. Kuma duk wanin dan Najeriya yayi Allah wadai da wadannan kalamai na wannan mata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da’ Yan Najeriya mazauna kasashen waje wato NIDCOM, Abdulrahman Balogun ya sa hannu, ya nuna goyon bayan matakan hukunci da za a dauka akan Amaka.
VOA Hausa