'Yansanda A Katsina Sun Kama Masu Safarar Makamai, Sun Kwato Alburusai Masu Rai
- Katsina City News
- 30 Aug, 2024
- 304
Zaharaddeen Ishaq Abubakar Katsina Times Agusta 30, 2024
Rundunar 'Yan sandan Jihar Katsina ta sanar da kame wasu mutane uku da ake zargi da safarar makamai, tare da kwato wani adadi mai yawa na alburusai masu rai.
Wadanda ake zargin sun hada da Ahmed Mohammed Kabir, Mannir Musa, da Aliyu Iliya, wadanda aka kama a ranar 29 ga Agusta, 2024, a garin Dutsinma, yayin da suke kokarin kai wa 'yan bindiga da ake zargi alburusai guda 740 a dajin Yauni.
Bincike na farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun samo wadannan alburusai ne daga Jihar Nasarawa domin kai wa wani jagoran 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Harisu, wanda har yanzu ba a kama shi ba.
A wani samame daban, rundunar ta kama wasu mutum uku da ake zargi da zama 'yan kungiyar fashi da makami, Abubakar Ibrahim, Abdullahi Nafi'u, da Adam Musa, da ake zargi da aikata fashi da makami a karamar hukumar Baure ta Jihar Katsina.
Wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Rundunar 'yan sandan ta yaba da kokarin jami’anta kuma ta tabbatar wa da jama’a kudirin ta na ci gaba da yaki da 'yan bindiga da masu safarar makamai a Jihar Katsina da sauran wurare.