Kungiyar Marubuta ta Kasa Reshen Katsina Ta Gudanar da Taron Ranar Hausa ta Duniya

top-news

A ranar Lahadi, 25 ga watan Agusta, 2024, Kungiyar Marubuta ta Kasa reshen jihar Katsina ta gudanar da taron tunawa da Ranar Hausa ta Duniya a dakin taro na Makarantar Horas da Koyon Sana'o'i da ke Kerau, cikin garin Katsina.

Taron ya samu halartar manyan mutane da suka hada da Uban Kungiyar, Farfesa Dr. Aliyu Kankara; Sarkin Aikin Kasar Hausa, Injiniya Kabir Ya’u Yamel; Alhaji Malam Kabir, tsohon shugaban kungiyar na kasa; da Malam Abdulkadir Mu’azu Isa Fago, mawallafin littafin "Sharri Kare Ne", da sauransu.

A taron, an yi bitar irin gudunmawar da marubuta ke bayarwa wajen bunkasa harshen Hausa a duniya, ta hanyar fassara rubuce-rubucen Larabci zuwa Hausa da amfani da yaren Hausa wajen koyar da yara karatu da sana’o’i. Malam Salisu Hafijo ne ya gabatar da wannan bayani.

Uban Kungiyar, Farfesa Aliyu Kankara, ya yi sharhi kan littafin "Sharri Kare Ne" na Malam Abdulkadir Mu’azu Isa Fago.

Sarkin Aikin Kasar Hausa, Injiniya Kabir Ya’u Yamel, ya bayar da shawarwari ga marubuta kan ci gaban harshen Hausa tare da yada shi zuwa wuraren da bai kai ba. Haka kuma, ya bukaci marubutan da su sanya al’adun Hausawa da zamantakewarsu cikin rubuce-rubucensu.

A nasa jawabin, tsohon shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Malam Kabir, ya yi kira ga marubuta da su kiyaye al’adun Malam Bahaushe tare da bin ka’idojin rubutun Hausa a ayyukansu. Sannan ya jinjinawa marubutan bisa kokarinsu na rike harshen Hausa.

Taron ya samu halartar dimbin mambobin kungiyar daga sassa daban-daban na jihar.

NNPC Advert