MARTANIN NNPC GA ZANCEN TSOHON MATAIMAKIN SHUGABAN KASA ATIKU ABUBAKAR
- Katsina City News
- 24 Aug, 2024
- 221
SANARWA ga manema labarai:
Fassarar Ibrahim Musa
By Katsina Times
An jawo hankalin kamfanin NNPC Ltd kan wata sanarwa da Mista Paul Ibe, mai baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Alhaji Atiku Abubakar ya sanya wa hannu. A cikin sanarwar, an ambato tsohon mataimakin shugaban kasar ya koka da "mallake kamfanin mai na NNPC da wasu gungun ke yi a kusa da shugaban kasar na yanzu suka yi".
An kuma ruwaito shi cewa ya lissafo ci gaba da rike Mista Mele Kyari a matsayin babban jami’in kamfanin na NNPC a matsayin diyya kan zargin mallakar NNPC Retail Ltd ta hanyar OVH, inda ya ce Mista Wale Tinubu na da kashi 49% na hannun jari.
Ya kuma yi zargin cewa yarjejeniyar saye da kamfanin NNPC Retail Ltd ta hanyar OVH na cikin wani gagarumin shiri da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na cudanya sha’anin kasuwanci na kashin kansa a cikin harkokin kasuwancin Nijeriya a matakin tarayya.
Kamfanin NNPC Ltd yana son saita bayanan daidai da wadannan bayanan:
1. Mu kamfani ne mai mayar da hankali kan kasuwanci da samun riba wanda kwararru ke tafiyar da shi, wadanda suka himmatu wajen karawa kasa alheri.
2. Shawarwarin zuba jarurruka na Kamfanin NNPC Ltd, an kayyade su ne bisa la’akari da ingancin kasuwanci da kuma amfanin kasa.
3. A lokacin da NNPC Ltd ta mallaki OVH a shekarar 2022, Oando (wanda Mista Wale Tinubu ke da hannun jari mai kauri), ya karkatar da kudadensa na OVH ga sauran abokan hulda guda biyu - Vitol da Helios. Oando a zahiri ya fara karkatar da shi a cikin 2016, tare da Vitol da Helios sun shigo a matsayin abokan haɗin gwiwa, wanda ya haifar da canjin suna daga Oando zuwa OVH. A cikin 2019, Oando ta karkatar da hannun jarinta daga OVH wanda ya haifar da Vitol da Helios suna rike da 50% na daidaiton jarin.
4. Bayan mallakar OVH da NNPC Ltd ta yi, dukkan su NNPC Retail Ltd da OVH sun zama rassa na NNPC Ltd. Duk da haka, bisa la’akari da shawarwari na ƙwararru da kuma ingantaccen tsarin kasuwanci, NNPC Ltd ta zaɓi haɗa NNPC Retail Limited zuwa OVH, sannan ta riƙe NNPC Retail Limited a zaman sunan kamfani bayan haɗewar.
5. An kammala matakin farko na hade kamfanin NNPC Retail Ltd da OVH, kuma ana ci gaba da canza sunan kamfanin NNPC Retail Ltd.
6. Sabanin kururuwar da aka yi na karya, Wale Tinubu ko Shugaban kasa ba su da wani hannun jari sayen OVH.
7. A matsayinsa na dan kasuwa, ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasa ya sani cewa inganci a harkokin kasuwanci yana da kyau a auna shi ta hanyar ma'aunin riba da nasarar da aka samu, maimakon la'akari da rade-mara tushe.
8. Mahukuntan kamfanin NNPC a karkashin jagorancin Mista Mele Kyari, sun yi kokari matuka wajen bunkasa arzikin kamfanin kamar yadda aka nuna a cikin bayynin harkokin kudade na 2023 na Kamfanin (2023 Audited Financial Statement (AFS), inda ya bayar da rahoton Naira tiriliyan 3.3 a matsayin riba bayan haraji.
9. Kamfanin NNPC Ltd a matsayinsa na mai yin kasuwanci ba shi da sha'awar siyasa, kuma zai ci gaba da gudanar da kasuwancinsa cike da himma wajen samar da alheri ga kasa da kuma samar da kima don amfanin duk masu jari. NNPC Ltd za ta bijirewa duk wani yunƙuri na jawo Hukumar da Gudanarwarta cikin siyasar bangaranci.
Olufemi O. Soneye
Babban Jami'in Sadarwa na Kamfanin
Kamfanin NNPC Ltd.
Abuja.