KIWON LAFIYA; 7.0. CIWON ZUCIYA ....ALAMOMIN CIWON ZUCIYA

top-news

Su ne kamar haka:
- A yayin da mutum ya kamu da wannan ciwo, zuciyarsa za ta kasa yin aikinta kamar yadda ya kamata, watau ta kasa harba wadataccen jini ga sassan jiki.

ABUBUWANDAKE KAWO CIWON ZUCIYA
Akwai abubuwa da yawa, wadanda ke haddasa ciwon zuciya. Wasu daga cikinsu su ne kamar haka:

1. Dadewa da fama da rashin wadatar jini a jiki (anemia). Idan hakan ta faru, zuciya za ta yi kokari domin ciko aikinta, watau harba jini ga duk sassan jiki, to amma ba isasshen jinin da zata harba. Saboda haka daga nan zuciyar sai ta zamo mai rauni, har ma daga karshe ta kasa gudanar da aikin nata.
2. Faruwar wata kofa ko kafa a cikin zuciya.
3. Ciwon da ke kama kafofin zuciya (wanda ta nan ne jini ke shige da fice a cikin zuciya).
4. Ciwon nan na makoko.
5. Wasu kwayoyin cuta wadanda ke zaune a cikin zuciya.
6. Hawan jini.

 7.2 ALAMOMIN CIWON ZUCIYA
Alamomin ciwon zuciya su ne kamar haka:
- Tari, da fitar da majina mai gauraye da jini.
- Rafafuwa za su kumbura.
- Jiyojin wuya za su fito.
- Kumburewar saifa.
- Amai (maiso).
- Tashin zuciya.
- Kasala.
- Ciwon kai.
- Akan samu matsala wurin numfashi a lokacin da mai fama da ciwon ya kwanta.

8.0 CUTUKKAN DA KAN KAMA HANTA
Cutukkan da kan kama hanta sun kasu kashi-kashi inda a cikin su akwai:

8.1 Kumburin hanta ta daya (hepatitis A)
Wannan cuta ta kan zauna cikin jikin dan-Adam har kimanin tsawon kwanaki sha biyar zuwa hamsin (15-50) kafin jiki ya fara nuna alamominta.

 ALAMOMIN WANNAN CUTAR
Alamomin wannan cuta su ne kamar haka:
1. Zazzabi wanda ke farawa sannu a hankali.
2. Kalar jiki.
3. Tashin zuciya, musamman a yayin da mutum ya zo cin abinci.
4. Rashin sha'awar cin abinci.
5. Amai (maiso).
6. Ciwon kai.
7. Fitsari zai zamo mai kalar kasa-kasa.
8. Daga nan sai alamun farar masassara. Kuma ita wa alama tana faruwa ne kwana uku zuwa bakwai (3-7) da nuna alamomin ita wannan cuta.

8.2 Kumburin hanta na biyu (hepatitis B)
Ita kuma wannan cutar ta fi dadewa a cikin jiki, inda ta ke daukar kimanin kwanaki arba'in da biyar zuwa dari da tamanin (45-180).

ALAMOMIN WANNAN CUTAR
Alamomin wannan cuta su ne kamar haka:
1. Zazzabi wanda ke farawa sannu a hankali.
2. Kalar jiki.
3. Tashin zuciya, musamman a yayin da mutum ya zo cin abinci.
4. Rashin sha'awar cin abinci.
5. Amai (maiso).
6. Ciwon kai.
7. Fitsari zai zamo mai kalar kasa-kasa.
8. Daga nan sai alamun farar masassara. Kuma ita wa alama tana faruwa ne kwana uku zuwa bakwai (3-7) da nuna alamomin ita wannan cuta.

8.3 YADDA AKE GANE CUTAR
Ana gane ta, ta hanyar alamomin da na yi bayani a kan su. Ta hanyar auna jini a asibiti domin gane kwayoyin cutar.

8.4 YADDA ZAA KULA DA MARAR LAFIYA
Akasarin masu fama da irin wannan rashin lafiyar ana kwantar da su asibiti. Sannan kuma a keɓe su don gudun yada cutar ga sauran marassa lafiya. Su ma masu aikin jinya sai sun kula da kyau wajen kula da wannan marar lafiya domin kare kawunansu daga daukar cutar.

1. Ana yi masu karin ruwa tare da zuba allurar nan mai sa cin abinci (B. complex) a ciki.
2. Idan aman ya tsaya za a bada abinci mai sa gina jiki. Misali wake, ko zogala ko wanda ke sa karfin jiki. Misali tuwo, ko doya, ko dankali. Sannan ba za a ba su mai dauke da kitse ba, misali man gyada, buluban da dai sauran su.
3. A tafasa duk kayan da aka yi ma wannan marar lafiyar aiki da su. Misali allura, da zarar an yi amfani da ita, sai a zubar da ita.

To, da zarar an ga wadannan alamomi sai a hanzarta zuwa asibiti mafi kusa, domin neman magani. Allah Ya sa mu dace: amin.

Daga Littafin Kula Da Lafiya Na Safiya Ya'U Yamel

NNPC Advert