Gwamna Radda Ya Fara Ziyarar Neman Jari a Kasar Sin
- Katsina City News
- 18 Aug, 2024
- 441
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
A kokarin karfafa huldar kasashen waje da jawo jarin kasashen duniya, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyar zuwa Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin.
Gwamna Radda tare da manyan jami'an gwamnati sun fara wannan ziyara daga 18 ga Agusta zuwa 23 ga Agusta, inda za su bincika damar zuba jari da kuma karfafa huldar kasashen biyu. Gwamnan ya iso filin jirgin sama na Daxing da ke birnin Beijing, inda Mr. William Lui ya tarbe shi, wanda zai karbi bakuncin tawagar.
A cikin tawagar akwai Sakatarensa na Musamman, Hon. Abdullahi A. Turaji; Kwamishinan Noma da Raya Dabbobi, Farfesa Ahmed Mohammed Bakori; Kwamishinan Ciniki, Kasuwanci da Zuba Jari, Alhaji Adnan Na Habu; da Babban Mashawarcin ziyarar, Mr. Haroun Abba Gana.
A lokacin ziyarar, tawagar daga Katsina za ta gana da jami'an gwamnatin kasar Sin, masu zuba jari da kuma masana'antun kera kayan aiki masu nauyi da na aikin gona. Wannan ziyara tana kara tabbatar da aniyar gwamnatin jihar Katsina na hada kai da kasashen waje domin bunkasa tattalin arzikin jihar.
Manyan bangarorin da tawagar za ta mai da hankali a kansu sun hada da samar da makamashi, musamman bangaren hasken rana, babura masu amfani da wutar lantarki, da kuma masana'antun hada kayan aiki. Haka kuma, za su ziyarci manyan kamfanonin kasar Sin kamar Sinotruck International, Jinan Zhongnihaihe Imports and Exports Trading Co. Ltd., da Cibiyar Bunkasa Tattalin Arziki ta Kasar Sin da ke lardin Shandong.
Wannan ziyara ta zama aikin farko na Gwamna Radda tun bayan dawowarsa daga hutun da ya dauka na wata daya, yayin da Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal Jobe, ya kasance a matsayin mukaddashin gwamna.
Gwamnatin Jihar Katsina tana da kwarin guiwar cewa wannan ziyara za ta haifar da gagarumar alaka da jarin da zai amfani bangarorin noma da masana’antu na jihar, wanda a karshe zai kawo ci gaba ga al’ummar Jihar Katsina.