ZARGIN KARA KUDIN TAKIN GWAMNATI A FUNTUA ....Da Kashe Kudin ba tare da bin ka'ida ba?
- Katsina City News
- 11 Aug, 2024
- 453
Jaridar Katsina Times ta samu korafe-korafe daga wasu 'yan Kwamitin Rarraba Taki da Gwamnatin Katsina ta tanada domin rabawa manoma a farashin rangwame. An yi zargin cewa an kara farashin takin fiye da yadda gwamnatin ta bayar da umarni, sannan an ce kudin da aka tara daga karin farashin an kashe su ba tare da bin ka’ida ba.
Wasu daga cikin 'yan kwamitin sun bayyana cewa gwamnati ta bayar da buhunan taki dubu goma sha tara domin rabawa manoman karamar hukumar Funtua, kuma ta umarci a sayar da shi akan naira dubu ashirin da biyar kowanne buhu. Duk da haka, masu zargin sun ce an kafa wani kwamiti a karamar hukumar Funtua domin rarraba takin, amma mutum daya ne ya yi amfani da damar tafiyar da dukkan al’amuran, ba tare da amincewar mafi yawan membobin kwamitin ba.
Masu korafin sun yi zargin cewa mutumin ya kara farashin takin sama da yadda gwamnatin ta ayyana, kuma an samu karin naira miliyan goma sha tara a kan yadda aka tsara. Haka kuma, sun ce kudin da ya kara ba a ba manoma wani rangwame ba daga gwamnati. Sannan, bayan an tara kudin da aka samu daga karin, an ce mutumin ya rika ba wasu daga cikin 'yan kwamitin kudi kamar alawus, wasu sun samu dubu dari, wasu sun samu fiye da haka, yayin da wasu ba su samu ko sisi ba.
Wakilan Jaridar Katsina Times sun tabbatar da cewa an bai wa karamar hukumar Funtua taki kuma an kafa kwamiti domin rarrabawa, kamar yadda aka yi a sauran kananan hukumomi. Sun kuma tabbatar da cewa an kara farashin takin fiye da yadda gwamnati ta umarce su, kuma an samu kudin karin fiye da naira miliyan goma sha tara.
Bayan tabbatar da wannan, editan jaridar ya tuntubi wanda ake zargi, Rabiu Adamu. A hirar da ya yi da jaridar, Rabiu ya tabbatar da cewa an ba su taki kuma an ba shi amanar sayarwa tare da sauran 'yan kwamitin da gwamnatin jaha ta nada a Funtua. Yace, an yi taro na farko inda aka tattauna yadda za a raba takin kowace mazaba, yadda za a dauko shi daga wurin ajiya, da kuma yadda za a gudanar da aikin kwamitin ba tare da taimakon gwamnati ba. Saboda haka, Rabiu ya ce an amince da kara kudin domin gudanar da ayyukan da suka shafi rabon takin, kuma ya yi hakan ne tare da amincewar 'yan kwamitin, ba don kansa kadai ba.
Rabiu ya kara da cewa kudin da aka tara daga karin farashin an yi amfani da su wajen aiwatar da duk wasu ayyuka da suka shafi kai taki zuwa duk mazabun da kuma sauran ayyukan da suka taso. Ya ce ba a raba kudin daidai ba, an raba ne bisa ga irin kokarin da kowa ya yi a lokacin aikin.
A karshe, Rabiu ya tabbatar da cewa akwai wasu daga cikin 'yan kwamitin da ba su halarci ko da taro guda ba, don haka ba su amfana da wani abu ba. Ya kuma yi ikirarin cewa duk yadda aka kashe kudin yana da su a rubuce kuma ya ajiye su domin duk wanda yake bukatar gani ya tabbatar.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.taskarlabarai.com.ng