Gwajo-gwajo Ya Taya Masari Murnar Samun Muƙamin Shugaban Hukumar Gudanarwar Na Asusun TETFUND

top-news

Babban mai baiwa gwamna shawara akan harkokin siyasa Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya taya tsohon gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari murnar samun muƙamin shugaban hukumar gudanarwar na asusun bunƙasa ilimin manyan makarantu (TETFUND)

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamna shawara akan harkokin siyasa Hon Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya fitar aka rabawa manema labarai a Katsina.

Hon. Ya'u Gwajo-gwajo ya ƙara da cewa baiwa Masari wannan muƙami tamkar an ɗora ƙwarya ne a gurbin ta, saboda kaunarsa a ɓangaren ilimi.

'Ina iya tunawa, Masari a matsayin sa, na gwamnan jihar Katsina ya baiwa bangaren ilmi mahimmanci na ɗaya wanda hakan ya haifar da gagarumin sauyi a ɓangaren ilimin firamare da da sikandire da kuma manyan makarantun gaba da sikandire." Inji shi 

Hon. Ya'u Gwajo-gwajo ya bayyana cewa a tsawon shekaru takwas da Masari ya yi a matsayin gwamnan jihar Katsina ya yi ayyuka daban-daban na raya kasa a manyan makarantun gaba da sikandire wanda ya taimaka wajen kyautata yanayin koyo da koyarwa a manyan makarantun.

Ya kuma cigaba da cewa baiwa Masari muƙamin shugaban hukumar gudunmawar ta asusun bunƙasa manyan makarantun gaba sikandire TETFUND ya nuna irin hangen nesan shugaba Tunibu na ƙoƙarin bunƙasa ɓangaren ilimi a Nijeriya 

Haka kuma Hon. Gwajo-gwajo ya lura cewar Aminu Bello Masari yana da masaniya akan abinda ya shafi shugabanci da dabirun da zai iya canza tsarin wannan hukuma zuwa wani mataki a fannin ilimi.

Daga karshe ya yi kira ga shugabannin da ma'aikatan wannan asusu da sauran masu ruwa da tsaki da su baiwa sabon shugaban hukumar gudunmawar Aminu Bello Masari goyan baya domin samun nasara akan wannan sabon muƙami.

NNPC Advert