Tatsuniya ta 43: Labarin Dankutungayya
- Katsina City News
- 10 Aug, 2024
- 279
Gatanan-gatananku
A wani gari mai suna Rakumawa, wani mutum ya ke zaune tare da matarsa da 'ya'yansu goma sha daya. A wata rana, matar ta haifi da namiji, wanda ya zama da goma sha biyu. Da aka haifi yaron, sai ya yi magana da uwarsa: "Kada ku yi wahala wajen radani suna, sunana Dankutungayya." Ya kara da cewa, "Kuma ragona kada a yanka, a bar shi don ni."
Iyaye suka bi wannan umarni, kuma jama'ar gari suka yi mamaki sosai da abin da wannan yaro ya yi.
Wata rana, yayyen Dankutungayya suka shirya zuwa gidan wata mata da suka saba zuwa hira. Sai Dankutungayya ya ce zai bi su, amma babban yaya ya hana shi. Duk da haka, bayan sun tafi, ya bi su a baya. Da suka isa gidan, matar ta yi musu maraba, ta shimfida musu wurin zama, ta kawo musu abinci mai dadi, suka ci, sannan suka fara hira. Amma ba su san cewa matar nan Dodanniya ce ba.
A kullum suna zuwa gidan suna hira, sannan su kwanta barci a wurin, Dodanniya kuma tana tashe su da safe su tafi gida. Ashe duk dabara ce ta ke yi don su saki jiki da ita, domin wani rana ta cinye su.
A wannan dare, Dankutungayya yana kallon abinda ke faruwa, sai ya lura cewa Dodanniya tana tafiya a sanda, tana dauke da wata sharbebiyar wuka. Ya fara yin tari don ya hana ta kusantar yayyensa. Amma tana dawowa da wuka, sai ya sake yin tari. Da ta ga lamarin yana nan, sai ta koma, sannan ta sake dawowa. Wannan karon, ta tambaye shi: "Kai, dan samari, ba ka barci ne?"
Ya amsa da cewa, "Ba na barci idan ba a kan rairayin korama mai sanyi ba."
Da ta ji haka, sai ta tafi neman rairayi. Da ta fita, Dankutungayya ya fito da magani, ya zuba a cikin wuta, sai hayaki ya tashi. Duk 'ya'yan Dodanniya da yayyensa suka yi nauyin barci. A cikin sauri, Dankutungayya ya tube wa 'ya'yan Dodanniya kayan jikinsu, ya sanya wa yayyensa, sannan ya kwanta.
Da Dodanniya ta dawo da rairayin korama, sai Dankutungayya ya ce: "Yawwa, na gode. Yanzu zan yi barci." Tana jin haka, ta dauki wukarta ta yanke duk 'ya'yanta tana tunanin 'yan'uwan Dankutungayya ne. Amma ta bar shi don yana karami.
Da Dodanniya ta fita, Dankutungayya ya sake barbada magani a kan wuta. Hayaki ya mamaye dakin, ya tashi yayyensa ya ce su gudu gida. Su kuma suka sulale suka gudu.
Da gari ya waye, sai Dodanniya ta zo don tattara wadanda ta yanka. Dankutungayya yana gani sai ya kira ragonsa, ya ce: "Wadannan fa 'ya'yanki ne kika yanka, ba 'yan'uwana ba." Ragon kuwa ya kama sukuwa da Dankutungayya a bayansa, ya bar Dodanniya cikin bakin ciki.
Dodanniya ta dauko magurjinta ta buga wa 'ya'yanta su zama tumakai, sannan ta soye suka ci. Daga nan ta yi alkawari cewa sai ta rama abin da Dankutungayya ya yi mata.
Bayan 'yan kwanaki, sai Dodanniya ta je bakin garin su Dankutungayya ta rikide ta zama kanya kuma ta haifi 'ya'ya da yawa, har sun kusa nuna. Cikinsu suka dinga kadawa suna sha. Wata rana yaran gari da yawa suka ga kanyar sai suka yi murna. Da ta nuna, wasu daga cikin yaran suka hau kanta suna diba. Da Dodanniya ta ga haka sai ta tashi sama da su, ba ta tsaya ba sai a gidanta. Nan da nan ta gaya wa autarta cewa nama tukwane sai Dankutungayya ya ji labarin abin da ya faru, sai ya rikida ya zama dan maraki, ya je gidan Dodanniya. Da zuwansa sai ya fara cin shuke-shuken da ke gidan, yana yi mata barna. Yana cikin wannan barna sai Dodanniya ta ce wa yaran da ta sato, su je su kori dan marakin mai yi mata barna.
Da suka ga sun doshe shi, sai ya ki gudu; amma da suka zo dab da shi, sai ya dan gudu ya dan matsa gaba kadan kuma ya ci gaba da barna. Yaran kuma suka dan matsa kusa da shi, ya dan kara gaba kadan. Haka dai ya dinga jan su, har sai da suka yi wa Dodanniya nisa. Sai ya rikide ya zama mutum, ya ce da yaran nan su hanzarta su gudu. Ya jaddada musu cewa idan ba su gudu ba, Dodanniya za ta cinye su. Da suka ji haka, sai suka sheka da gudu, suka koma garinsu, suka gaya wa iyayensu abin da ya faru.
Shi kuwa Dankutungayya sai ya hau ragonsa, ya koma gidan Dodanniya. Da ya tabbatar ta gan shi, sai ya yi mata gwalo ya ce mata: "Na kubutar da yara daga sharrinki, sun koma wurin iyayensu. Ni ne Dankutungayya na yi miki gayyar tawa, wadda ba za ki iya ramawa ba har abada." Wannan abu da Dankutungayya ya yi wa Dodanniya da maganar da ya gaya mata, suka sa ta shiga tunani da kulla yadda za ta dauki fansa a kansa.
Ana nan, sai Dodanniya ta rikide, ta zama mace kyakkyawar gaske, ta dauki wani adudu ta je cin kasuwa. Masoya suka yi ca a kanta, kowa yana so ya aure ta amma ta ce ba wanda za ta aura, sai wanda ya bude wannan adudun. Samari da yawa suka gwada, amma duka suka kasa.
Bayan 'yan kwanaki, har samari sun fid da rai, sai daya daga cikin yayyen Dankutungayya ya ji labari, ya bincika inda take a kasuwa ya je kuma ya gan ta, sai ya ji yana son ta. Ita kuma Dodanniya ta gane shi, saboda haka sai ta yi tsafi ta yadda idan ya gwada bude adudun zai bude. Da zuwansa kuma ya gwada sai adudun ya bude, mutane suka yi ta mamaki, shi kuma ya yi murnar samun kyakkyawar mata. Aka daura aure, ba ta jima ba ta tare a gidansa. Amma bayan 'yan kwanaki sai ta kwakwale wa mijin ido daya, ta tafi da shi ta bar shi da jinya.
Dankutungayya da jin wannan aika-aikar ya tabbatar da cewa Dodanniya ce. Don haka ya kudiri aniyar sai ya dauko fansar abin da ta yi wa yayansa. Sai ya rikida ya zama Bafulatana, ya dauki nono, ya je gidanta talla. Da isarsa sai autar Dodanniya ta fito ta saya. Shi kuma ya yi mata araha. Kullum sai ya kai tallar nono, Dodanniya ba ta gane gogan ne ba. Da haka har Dodanniya ta saba da Bafulatana kwarai da gaske.
Wata rana sai Bafulatana, watau Dankutungayya ya zo gidan Dodanniya a fusace. Dodanniya ta tambayi Bafulatana dalilin fushinta, sai ta ce: "Wani mutum wai shi Dankumale yake zuwa yana kashe musu shanu. Ga shi yanzu duk sun kusa karewa." Dodanniya ta ce: "Ke ba sunansa Dankumale ba, sunansa Dankutungayya. Mugun mutum ne. Ba shanunku kadai ba, ku kanku ma ku yi hankali da shi. Ni 'ya'yana goma sha daya ya sa na kashe. Kwanan nan ma na kusa makantar da dan'uwansa. Kin ga idon yayansa da na kwakule."
Sai Bafulatana ta ce: "Tir, da ganin idon lalatacce." Sai Dodanniya ta ce: "Yau saura kwana uku ma in ba kyanwata idon mugun ta cinye." Bafulatana ta ce: "Kash, da idon nan zai yi wa kanena daidai da kin ba ni shi. Shekaran jiya saniya ta harbi idonsa daya ya fashe ya tsiyaye." Cikin ɗoki da ƙeta Dodanniya ta ce: "Af, don wannan ai sai in ba ki." Da jin haka sai Bafulatana ta yi farat ta ce: "Ai ko na gode."
Dodanniya ta ƙara yi wa Bafulatana gwaninta, sai ta gaya mata yadda za ta sa masa idon ta ce: "A nemo kwaikwayen Kifi guda bakwai da hantar bakin Kare, da Kiyashi guda bakwai da kaucin Marke, a shanya su bushe, sai a nika, a rinka sa masa a gurbin idon har kwana uku. A rana ta hudu, sai a sa idon, zai zauna daram."
Bafulatana, watau Dankutungayya, ta amshi ido, ta yi godiya. Da ta gusar kadan, sai ta tube kayan Fulani, sai ga Dankutungayya ya bayyana. Sai ya yi wa Dodanniya gwalo, ya ce: "Kin ga, ni ne Dankutungayya." Sai ya yi wani hatsabibanci ya bata, Dodanniya ta daina ganinsa. Bai tsaya a ko'ina ba sai gida. Da ya isa ya yi yadda Dodanniya ta kwatanta masa, idon yayansa kuma ya zauna daram, kamar ba a taba kwakule shi ba.
Kannan kuma sai Dodanniya ta rikida ta zama Kyanwa. Ta kama hanya ba ta tsaya ko'ina ba sai a gidan su Dankutungayya. Da shigarta sai ta iske yana barci; sai ta laɓa, ta kai kusa da shimfidarsa. Sai ta yi wani karatu irin na tsafinta, ta tofa masa a fuska, sai ya zama Bera sai ta dauke shi ta kai gidanta, ta sa shi a kuryar daki. Daga nan ta yi masa wani tofin, ya koma mutum. Ita kuma ta rikida ta zama mutum. Sai ta harare shi, fuskarta ba dariya, tana cike da fushi. Ta ce: "Dankutungayya, yau fa ga ni ga kai, karyarka ta kare." Dankutungayya bai tsorata ba, kuma bai ce mata komai ba.
Can da Dodanniya ta dan huta, sai ta sa autarta tsaron Dankutungayya, ita kuma ta kama hanyar kasuwa sayen kayan yaji wanda za ta dafa shi da shi. Tafiyarta ke da wuya sai Dankutungayya ya yi wa 'yar auta dabara, ya karbe kayan jikinta ya sa, ita kuma ya sanya mata nasa. Can sai ya ji motsin Dodanniya ta dawo, ya zabura, ya tarye ta yana kwaikwayon maganar 'yar auta, yana yi mata maraba. Bayan wani dan lokaci kuma sai ga yar autar a cikin kayan Dankutungayya, tana yi mata maraba. Sai Dankutungayya ya dubi Dodanniya ya ce mata: "Ga munafukin nan Dankutungayya yana cewa shi ne ni 'yar autarki har da cewa, 'Sannu da zuwa inna' karyarsa ta kare."
Sai Dodanniya ta ce: "Lallai kam; bar ni da lalatacce!" Nan take ta yi wuf, ta shako 'yarta, ta sa wuka ta yanka, kurunkus. Tana gama yanke autarta, sai Dankutungayya ya buga tsalle gefe ya kwance zannuwan da ya daura, ya dubi Dodanniya ya ce: "Yar auta kika yanka, ni ko ni ne Dankutungayya, gwanin gayya. Na yi miki gayyar tawa!"
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa:
1. Kaikayi koma kan mashekiya.
2. Kaunar juna da son 'yan'uwa kan ƙara dankon zumunci.
3. Mugunta fitsarin fako ce, kan wanda ya yi take komawa.
4. Dan'uwa rabin jiki.