Ziyarar Kwamishinan Ayyuka na Katsina Zuwa Mazabu 11 a Ingawa
- Katsina City News
- 04 Aug, 2024
- 349
Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar Katsina, Engr Dr. Sani Magaji Ingawa, ya ziyarci mazabu 11 dake karamar hukumar Ingawa a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli.
A lokacin ziyarar, Kwamishinan ya samu ganawa da shugabannin jam’iyya, dattawa, matasa maza da mata, da kuma iyayen kasa, magaddai da limamai na kowane mazaba. Haka zalika, ya gana da wasu manyan kungiyoyi dake garin Ingawa, sannan ya ziyarci makarantun allo tare da kai tallafin abinci don rage musu radadin da ake ciki.
A cikin jawabansa, Kwamishinan ya godewa al’ummar karamar hukumar Ingawa bisa irin goyon bayan da suka ba su tun daga lokacin da suke yakin neman zaben Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Dikko Radda, da sauran 'yan takarar jam’iyyar APC a zaben da ya gabata.