Muna Gudun Sabon Rikici a PDP Jihar Katsina - Hon. Majigiri

top-news


A ranar Asabar da ta gabata, jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta gudanar da wani taro mai muhimmanci na ƙara wa juna sani da tattaunawa game da halin da jam'iyyar take ciki, musamman dangane da zaɓen shugabannin jam'iyya a matakin mazabu wanda aka gudanar a wasu jahohi.

A cikin mahalarta taron akwai Hon. Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas Katsina), ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Mashi da Dutsi, kuma ɗaya daga cikin jigajigan PDP. Majigiri ya bayyana illar gudanar da zaɓen shugabanni alhalin maganar tana kotu, inda ya bada misali da jihar Plateau da ta yi asarar kujerun 'yan majalisar dokokin jihar saboda rashin bin umarnin kotu.

Ya yi gargadi ga duk wanda ke shirin jefa jam'iyyar PDP ta jihar Katsina cikin irin wannan hali da ta faɗa a jihar Plateau, saboda son zuciya da rashin bin dokoki. Hon. Majigiri ya tabbatar da cewa za su ci gaba da yaƙi har sai an bai wa kowane ɗan jam'iyya haƙƙinsa.

Taron ya samu halartar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Malam Mustapha Inuwa; tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP na ƙasa, Sen. Umar Tsauri; tsohon Sanatan Shiyyar Daura, Sen. Ahmad Babba Kaita; da Ma'ajin Jam'iyyar PDP na shiyyar Arewa maso yamma, H.E Rabi'u Gambo Bakori; da Hon. Salisu Uli, tare da dukkan shugabannin jam'iyyar PDP na ƙananan hukumomin jihar Katsina 34, da shugabannin mata da na matasa na tsagin, tare da sauran shugabanni.

NNPC Advert