Biyan Fansho Da Giratuti Na Biliyan 8: Hon Gwajo-gwajo Ya Jinjinawa Gwamna Dikko Raɗɗa

top-news


Mai Baiwa shawara akan harkokin siyasa Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya jinjinawa gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa bisa amincewa a biyan haƙoƙin ma'aikatan da suka ajiye aikin su daga Janairu 2020 zuwa Augusta 2023 kuɗin fansho da giratutin su har biliyan 8 

Bayanin haka na kunshe ne acikin wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Katsina 

Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya ce ya lura da cewa amincewa a biya waɗannan kuɗaɗai ya zo daidai lokacin da ake buƙatar su saboda yanayin na matsin tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasa, sai gashi waɗanda suka ajiye aiki za su karbi haƙoƙin su.

"Babu shakka wannan yunkuri da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi ya nuna matuƙar kulawar sa, akan sadaukarwa da jin dadin ma'aikata da waɗanda suka ajiye aiki" inji shi 

Ya ƙara da cewa biyan waɗannan kuɗaɗai na fansho da giratuti na cikin alkawaran da gwamna Dikko Raɗɗa ya yi lokacin yaƙin neman zaɓen inda ya ce idan Allah ya bashi kujerar gwamna zai biya su, kuma gashi ya cika.

Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya ce gwamna Raɗɗa ya zama mutum da ya maida hankali wajen cika alkawarin da ya ɗauka musamman wajen kula da jin dadi da walwalar ma'aikata da waɗanda suka ajiye aiki.

Daga ƙarshe ya yi kira ga ma'aikata da waɗanda suka ajiye aiki da sauran al'umma da suka goyi bayan tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnatin jihar Katsina karkashin Malam Dikko Raɗɗa domin ya samu nasara

NNPC Advert