TSOKACIN MASANA KAN GUDUNMUWAR DA SHUWAGABANNIN JIHADI SUKA BADA A KARNI A (19).

top-news

  Acikin karni na 19 ne Mujaddadi Shehu Usman Danfodio ya fara Kira da a kaddamar da Jihadi a Kasar Hausa don Jaddada addinin musulunci. Wannan Kira ya farune saboda halin da Kasar Hausa ta tsinci kanta a wannan lokacin na Mulkin Gadara, da danniya, da ganganci da Kuma rashin Imani, sannan da chakuda addinin musulunci da addinin Gargajiya, misali Bori da Tsahi da sauransu. 

   Marubuta da dama sunyi tsokaci akan Jihadin da Shehu ya kaddamar a karni na 19. 

    Kadan daga cikinsu sune. 

1. Danbatta (1979-6-7) ya bayyana cewa:
  
  " A Karni na Sha tara an samu wani Yunkuri na bunkasa Ilimi da yada addinin musulunci, da kauda jahilci da al'ada, da camfe-camfe a Kasar Hausa. Shuwagabannin Jihadi sun wallafe- wallafe- masu dinbin yawa na fannonin ilmi daban-daban da Larabci kamar su Tauhidi, da Fikihu da hukunce hukuncin Sharia da tsarin mulki da dai sauransu. 

2. Yahaya (1988:49) ya Jaddada cewa:

 Rubutattatun Wakokin Hausa sun Sami gagarumar bunkasa ta fuskar yawaita, da bazuwa a koina, da Kuma ingancin tsari da salon sarrafa harshe acikin karni na 19. Wannan kuwa ya samune saboda rabautar da Kasar Hausa ta yi da ayyukan da Mujaddadi Shehu Usman Danfodio da Jamaarsa sukayi wajen tashi tsaye kan gyaran addini, da yada ilmi, da kyautata halayen rayuwa wadanda suka gurbace a Kasar Hausa a wancan zamani 

3. Dan Gambo(2008;1) ya bayyana cewa;

  Mun samu bayanan yadda su Shehu Usman Danfodio da mabiyansa suka yi ta rubuta Wakokin Hausa da Ajami don yin wa'azi da sauransu, don yada addinin musulunci. 

4. JUNAIDU DA YAR'ADUA(2007:123-4) Sun bayyana cewa;

Hausawa sun fara kokarin rubuta Wakokin da sukan rera da baka bayan zuwan addinin Musulunci, Sai suka ci gaba da habaka , sukayi ta yawa a lokacin Jihadin Shehu Danfodio, don da sune Shehu da almajiransa suke amfani don yin wa'azi da jawo hankalin Jama'a ga daukar sahihan hanyoyin addini. To, bayan zuwan Turawa Sai  marubuta Wakokin Hausa suka Kara yawa, suka yi ta wallafa wakoki. Don haka a takaice zaa iya   raba Wakokin Hausa zuwa rabo biyu, Wakokin Karni na 19, wato Wakokin da aka rubuta lokacin Jihadi. Wakokin Karni na 20 wato Wakokin da aka rubuta lokacin zuwan Turawa, har zuwa yanzu. 

5. Shi kuwa Abdulkadir (2008-148-9); Ya bayyana cewa an haifi Abdullahi danfidio shekarar 1180 A. H./1766-7A. D. Shehu Usman Danfodio ya girmi Abdullahi, ya bashi shekara goma Sha biyu, kamar yadda yadda rubuta cikin littafinsa Tazyin Al- warakat. Abdullahi Danfodio ya fara neman ilimi karkashin mahaifinsa sannan ya tafi ga wasu masana na kusa Dana nesa. Wannan bawan Allah yakai  matuka wajen ilimi. Daga cikin Malaman da Abdullahi Danfodio ya yi Karatu a gabansu akwai Sheik Jibril Ibn Umar, shahararren Malami ne a Agades Kuma ya koyama Mujaddadi  Shehu Usman Danfodio. 

                A karkashin wannan Malami Abdullahi Danfodio ya karanci fannoni da dama na ilimin addinin Musulunci. Wannan ya ba shi damar yin rubuce-rubuce masu yawa musamman a kan mas'aloli da suka danganci addini da siyasa da mulki da Kuma wasu abubuwa da suka danganci rayuwar Musulmi. Bugu da Kari yayi sharhin Risalat ta Abi Zaid. Sannan ya taimaka wa Shehu Usman Danfodio dangane da ziyarar Garuruwa da dama a Kasar Hausa domin Jihadin gyara Musulunci a farkon karni na 19, zamanin da aka sami Kasar Hausa  karkashin  tafarkin mulkin gadara da ganganci da Kuma rashin Imani. Da dai sauransu. 

Sourse;

1. Al'adunmu;   Jounal of Current Reseach in African Studies. A publication of Katsina State History and Culture Bureau, in Collaboration with Faculty of Humanities, Ummaru Musa Yar'adua University, Katsina. Page 181-182. 

Alhaji Musa Gambo Kofar soro. 07-07-2024.

NNPC Advert