Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara Ya Samu Lambar Yabo Ta Kirkiro Ayyuka
- Katsina City News
- 08 Jul, 2024
- 451
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu lambar yabo ta ‘Ƙirƙirar Ayyuka’ a bikin bayar da lambar yabo ta ‘Kyautar Yabo Ta Yi Wa Al'umma Hidima’ (NEAPS) bisa ɗimbin ayyukan da gwamnatinsa ta ƙaddamar da kuma kammalawa a cikin shekara guda.
NEAPS wani shiri ne na kamfanoni masu zaman kansu da kuma ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF).
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce an gudanar da bikin karramawar na NEAPS ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata a ɗakin taro na fadar gwamnatin tarayya.
Sanarwar ta ƙara da cewa, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya ba Gwamna Dauda Lawal lambar yabon.
“A ranar Asabar ne aka karrama Gwamna Dauda Lawal da lambar yabo ta NEAPS saboda jajircewarsa na ƙoƙarin samar da nagartaccen sauyi, da kuma ƙoƙarin samar da al’ummar dimokuraɗiyya, da kuma gyara hukumomin gwamnati yadda ya kamata.
“Wasiƙar lambar yabon daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa an zaɓi Gwamnan Zamfara ne saboda ƙoƙarinsa wajen ƙirƙirar ayyukan ci gaban al'umma.
“An ba da lambar yabo ta shugaban ƙasar ne domin nuna godiya ga ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi na ɓullowa da kuma kammala ayyuka da dama cikin shekara ɗaya.”
Gwamna Lawal ya nuna jin daɗinsa da karramawar, inda ya bayyana cewa hakan zai zama kwarin gwiwa ga ci gaba da ƙoƙarin ceto da sake gina Zamfara.