Gwamnan Zamfara Ya Taya Al'ummar Jihar Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci

top-news


Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya aika da saƙon taya murnar shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1446H ga al'ummar jihar.

Cikin saƙon, Gwamna Lawal ya fatan sabuwar shekarar za ta zama mai albarka ga al'ummar jihar da ƙasa baki ɗaya. Ya hore su da su jajirce wajen addu'o'in neman zaman lafiya mai ɗorewa.

A wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, an bayyana cewa sabuwar shekarar lokaci ne na nazarin abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata, domin dunfarar ci gaba.

"Yau ɗaya ga watan Muharram, wanda ya kawo ƙarshen shekarar 1445H, kuma farkon shekarar musulunci ta 1446H.

"Wannan dama ce ba kawai ga al'ummar Zamfara ba, har ma ga dukkan al'ummar ƙasar nan, wajen dagewa da yin addu'o'i don samun zaman lafiya.

"Dukkan mu muna da muhimmin rawar da za mu taka wajen ci gaban jihar mu da ƙasa baki ɗaya.

"Ina yi wa jama'a fatan alheri da ci gaba mai amfani. Allah kare mana jihar mu ta Zamfara da Nijeriya baki ɗaya."

NNPC Advert