YAJIN AIKI: Hukumar Rarraba wutar Lantarki KEDCO Ta Rufe Babban Ofishin ta dake Kano

top-news

YAJIN AIKI: Ma’aikata sun rufe babban ofishin rarraba wutar lantarkin Kano

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

A bisa cika sharuddan yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da kungiyar kwadago ta Najeriya, kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa, ta fara a safiyar ranar Talata (yau), ta rufe babban ofishin kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano, dake kan titin gidan waya a cikin birnin Kano.

Idan dai ba a manta ba Kungiyar Kwadago ta ƙasa NLC a karshen taronta a ranar 31 ga watan Agustan 2023, ta yanke shawarar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.

Kungiyar ta umarci daukacin mambobinta da su fara yajin aikin daga ranar Talata 5 zuwa Laraba 6, 2023.

Yajin aikin na da nufin nuna adawa da janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.

Wannan baya ga ƙin samar da matakan da suka dace kuma masu inganci don rage tasirin wahalhalun tattalin arziƙin da ke haifar da cire tallafin.

Da aka tuntubi Shugaban Kamfanin Sadarwa na KEDCO, Sani Bala, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa yana bin umarnin kungiyar ta NLC.

Shi ma a nasa martanin mataimakin shugaban kungiyar NLC reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, wanda ke gudanar da aikin tabbatar da tsaro ya tabbatar da cewa ta rufe dukkanin ofisoshin gwamnati a jihar.

Ya kuma ce bankunan jihar su ma sun bi umarnin. Riruwai ya kuma ce zai nufi filin jirgin saman Mallam Aminu Kano domin tabbatar da bin umarnin NLC na cewa kada wani jirgi ya sauka ko tashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *