Yadda wasu maƙiya su ka shirya bayanan ƙarya a kan ɗan jarida, Shuaibu Mungadi
- Sulaiman Umar
- 30 Jun, 2024
- 421
Shuaibu Mungadi ɗan jarida da ke aiki a gidan telebijin na Farin wata wanda ya tsinci kansa a wani mummunar yanayi, biyo bayan da wata kafa mai suna ‘Zamfara News Letter’ ta ruwaito cewa ana zarginsa da yi wa ƙawar ƴarsa ciki.
Wannan labari ya ɗauki hankalin mutane kasancewar hakan abu ne da zai ɓata sunansa a cikin al’umma.
Wani bincike da kafar ta yaɗa daga wasu ƴan siyasa waɗanda ke harin mutanen da suka saɓa da su wajen ra’ayi, ya ce, Mungadi ya ƙulla mummunar alaƙa da ƴar Maijidda Labaran wanda haka ta kai ga yarinyar ta samu juna-biyu na wata uku.
Kafar ta ce Mahaifiyar yarinyar mai suna Maijidda Labaran, ta ce Mungadi ya yi amfani da damar kasancewarta ƙawa ga ƴarsa ta biyar.
A wani ɓangare kuma, binciken jaridar ‘Spectacles’ ya ce hoton da aka samu a rahoton ya ƙaryata zargin tare da nuna ƙarara hakan kasuwanci ne da kuma yaudara ta siyasa, don maganganu ne da basu da hujja sai dai kawai hakan wani makirce da kuma yunƙurin ɓata masa suna daga ƴan siyasa da yake ƙalubalantar munanan ayyukansu.
Kafar ‘Zamfara News Letter’ sananniya ce wajen yaɗa labaran ƙarya da sharri da ƙage wa mutane a madadin ƴan siyasa.
Jaridar ‘Spectacules’ ta buƙaci Mungadi da ya shigar da duk waɗanda ke da hannu cikin ɓata masa suna ƙara, domin doka ta yi aiki a kansu.
Shuaibu Mungadi shi ke jagorantar shirin ‘idon mikiya’ a gidan telebijin na ‘Farin Wata’ da kuma ‘Vision FM’.