MUNA AIKI SOSAI DON SAMAR DA RUWA A JAHAR KATSINA -inji Dakta Hassan Tukur Tingilin

top-news

..Me ya kawo matsalar  ruwa a birnin Katsina? 

Muazu Hassan @ Katsina Times 
Shugaban hukumar samar da Ruwan sha ta jahar Katsina, Alhaji Tukur Hassan Tingilin ya bayyana ma jaridun Katsina Times, cewar hukumar sa na aiki ba dare ba Rana domin samar da ruwan sha a birnin Katsina da kewaye da sauran sassan jahar baki daya.

Da ya ke zantawa da jaridun Katsina Times yace matsalar da aka samu kwanan nan na matsalar ruwa a birnin Katsina da kewaye yazo ne sakamakon ballewar wata gada a yankin Dutsinma wadda ake Kira da gadar Kagara.yace ballewar wannan gadar yazo ne sakamakon dibar yashi da akeyi a wajen, kuma ya haifar da zaizayar ruwa ta shafi fayif din dake kawo ruwa daga dam din zobe, zuwa Katsina.  

Tingilin, ya kara da cewa dole aka tsaida turo ruwa daga zobe domin sai an tace shi an kuma sa masa maganin kashe cuta an harbo shi, sai kashi  tamanin ya koma dam din kashi ashirin ya taho kuma bai isa koina sai ya tsaya.
Tingilin yace, muna daukar matakin gyara da kuma hana wannan dibar yashi dake cutar da al umma.

Tingilin yace matsalar Ajiwa kuma, ma aikatan kedco ke wani aikin akan layin wutar dam din , Wanda ya katse samun wutar da za a halbo ruwan  domin an yanke daga janareto da kuma Nepa saboda gyaran.

Tingilin ya kara da cewa gwamnan Katsina ya damu sosai akan matsalar ruwan dake damun al umma , har ya amince da duk wani tsari da hukumar zata kawo don a kawo karshen wannan yanayi.

Daga cikin abinda ya amince dashi har da sanya Dam din dake harbo ruwa su kara da tsarin amfani da hasken Rana don samun lantarkin da za a yi aiki dashi. Ya kara da cewa nan da lokaci kankane za a fara wannan aikin na kara amfani da hasken Rana don samun lantarki  a dam din Ajiwa.yace dam din zai zama yana iya amfani da Nepa, janareto sai kuma hasken Rana.

Tingilin yace, tunda na fara aiki, kullum ba zaune muke ba, ni da ma aikatana, kullum kowace Rana akwai abin da muke a wani Dam ko wani gari.Muna kuma samun cikakken goyon baya da karfin gwaiwa daga gwamnan Katsina.

Tingilin yayi riko ga kamfanoni da jama a su bada gudummuwar su ta kariya da kiyaye duk inda wani aikin hukumar yake, su kuma taimaka wajen biyan kudin ruwan da suke amfani dasu.

NNPC Advert