Shugaban Kasa Ya Kaddamar Da Babban Taron Tsaro A Jihar Katsina

top-news

A ranar Litinin, 24 ga Yuni, 2024, Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, tare da wasu manyan masu ruwa da tsaki na shiyyar Arewa maso Yamma, sun iso dakin taro na masaukin Shugaban Kasa dake fadar Gwamnatin Jihar Katsina domin halartar babban taro akan tsaro.

Taron, wanda aka shirya domin kaddamar da zaman lafiya da tsaro a Arewa maso Yamma, ya gudana ne a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda. Wannan taron hadin gwiwa da Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ya samu halartar gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma, tsoffin gwamnoni, shugabannin hukumomin tsaro, sarakuna, manyan 'yan kasuwa, da 'yan siyasa daga ko'ina cikin shiyyar.

Babban makasudin taron shi ne tattauna hanyoyin da za a bi domin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi shiyyar da sauran sassan kasar, matsalar da ke ci gaba da lakume rayukan al'umma da kuma asarar dimbin dukiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *