Katsina Ta Lashe Lambar Yabo Ta Mafi Kyawun Hukumar Inshorar Lafiya Ta Jiha Na 2024
- Katsina City News
- 23 Jun, 2024
- 681
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Jihar Katsina (KTSCHMA) ta samu lambar yabo ta "Mafi Kyawun Hukumar Inshorar Lafiya Ta Jiha Na Shekara Ta 2024" a bikin bayar da kyaututtuka na kasa da aka gudanar a Legas. Wannan shi ne karo na biyu da Katsina ke samun wannan lambar yabo, bayan samun nasara a shekarar 2022.
Jihar Katsina ta samu wannan yabo tare da wasu jihohi kamar Legas, Adamawa, Kano, da Anambra.
Hukumar KTSCHMA ta sami wannan nasara ne saboda tsare-tsarenta na kiwon lafiya da kuma matakan da ta dauka wajen inganta kiwon lafiya a jihar. An yaba da gudunmawar da gwamna da sauran masu ruwa da tsaki suka bayar wajen cimma wannan nasara.
Da yake mayar da martani game da wannan yabo, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gode wa duk wadanda suka bada gudunmawa wajen samun wannan nasara, ciki har da Kwamishinan Lafiya, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na KTSCHMA, da Darakta Janar tare da tawagarsa.
Gwamnan ya ce za su ci gaba da aiki tukuru don inganta kiwon lafiya ga mazauna Jihar Katsina.