Jinjina ga Gwamna Dauda Lawal daga Tsohon Gwamnan Bauchi
- Katsina City News
- 22 Jun, 2024
- 452
Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu ya jinjina wa Gwamna Dauda Lawal bisa ayyukan inganta tituna da ya aiwatar a Jihar Zamfara.
A ranar Juma'ar nan ne tsohon Gwamnan, wanda ya ke kuma tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP na ƙasa, ya ƙaddamar da wasu ayyukan tituna a babban birnin jihar, Gusau.
Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa titunan da Adamu Mu'azu ya ƙaddamar, sun haɗa da titin Freedom Square zuwa mahaɗar Nasiha Chemist; sai kuma wacce ta tashi daga Freedom Square zuwa gidan gwamnati; da kuma ta gidan gwamnati zuwa Lalan zuwa Gada Biyu.
Idris ya ƙara da cewa ayyukan titunan Freedom Square zuwa mahaɗar Nasiha Chemist da ta Freedom Square zuwa gidan gwamnati, kamfanin Ronches Nigeria Limited ne ya aiwatar da su; sannan shi kuma kamfanin Triacta Nigeria Limited ya aiwatar da titin da ya tashi daga gidan gwamnati zuwa Lalan zuwa Gada-Biyu.
Cikin jawabin sa wajen bikin, Gwamna Dauda Lawal ya bugi ƙirjin cewa tun da aka kafa Jihar Zamfara, shekaru 28 ke nan, sai yanzu ne Gusau ta cancanci a kirata babban birnin jihar.
“Zan fara da yi wa babban baƙon mu marhabin lale zuwa wannan biki. Wannan kuwa ba wani ba ne illa tsohon Gwamnan Jihar Bauchi kuma tsohon Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, mai girma Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu, CON. Har gobe abubuwan da ka kafa a matsayin ka na Gwamna da Shugaban PDP, zai zama abin koyi ga shugabanni masu tasowa.
“Babu shakka, dole ne mu yi wa Allah godiya mara iyaka bisa damar da ya ba mu na aiwatar da ayyuka. Uwa-uba, Allah ya ba mu damar cika alƙawuran Zamfarawa da muka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe. Ina ƙara jaddada aniyata ta sadaukarwa ga jihata a kowane lokaci.
“Don haka, bisa waɗannan ni'imomi na Allah, yau za mu buɗe hanyar da ta tashi daga Freedom Square zuwa mahaɗar Nasiha Chemist, Freedom Square zuwa gidan gwamnati, wanda kamfanin Ronches Nigeria Limited ya aiwatar; sannan daga gidan gwamnati zuwa Lalan Gada-Biyu, shi kuma kamfanin Triacta Nigeria Limited ne ya aiwatar. Waɗannan na ciki wasu ayyukan da gwamnatina ta aiwatar daga lokacin da muka hau mulki.
“Waɗannan ayyuka da muke ƙaddamarwa a yau, kashi na biyu ne a jerin ayyukan mu masu ɗimbin yawa. Da zarar mun kammala tsare-tsaren da muka yi na raya birane, to dukkan mu za mu iya bugun ƙirji mu kira Gusau a matsayin babban birnin jihar mu. Bugu da ƙari, za mu aiwatar da ayyukan more rayuwa a duk Ƙananan Hukumomin jihar nan 14.
“Da wannan ɗan taƙaitaccen jawabin, na ke farin cikin gayyatar tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmad Adamu Mu'azu, CON, ya zo ya buɗe waɗannan ayyukan da gwamnatina ta aiwatar a shekara ɗaya da na yi ina shugabantar jihar nan, a matsayin wani sashe na ayyukan raya birane."
Tun farko, Babban baƙo, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmad Adamu Mu'azu, CON, ya nuna matuƙar jin daɗin sa bisa waɗannan ayyukan na Gwamna Lawal, yana mai bayyana cewa shi shugaba ne mai ƙwazo da hangen nesa.
“A yau, ina mai alfahari da godiya ga Allah bisa ayyukan yabawa da Gwamna Dauda Lawal ya aiwatar.
"Babban al'amari na waɗannan titunan shi ne cewa an gina su da inganci kuma bisa tsarin yadda duniya ke tafiya. Zan iya tabbatar muku da cewa waɗannan hanyoyi ne masu ɗorewa."