BA ZAMU GAJIYA DA ROKON GWAMNATI BA KAN TA KAWO MANA DAUKI- Mazauna wasu Unguwanni a Garin Katsina
- Katsina City News
- 12 Jun, 2024
- 507
A yayinda yanayin damina keta kara kankama, Al'ummar dake zaune a unguwannin Sabuwar Dutsin-safe low cost da, Bayan gidan taki da malali sunyi roko ga Gwamnatin jihar Katsina akan tasamar musu da mafita akan wata matsala dake musu barazanar ga rayuka da dukiyoyinsu.
Wannan matsala itace ta rashin hanyoyin fitar da ruwa daga unguwar wadda hakan ke haifar da rugujewar gidaje da zaizayewar hanyoyi a shekara da shekaru musamman a lokutan damina.
A saboda hakane, shugabannin wadannan al'ummomi suka gudanar da ayyukan gayya Wanda zasu iyayi bakin karfinsu tareda taimakon masu hali a cikinsu, domin rage girman matsalar a bakin gwalgwado kafin daukin Gwamnati.
A bayan kammala wannan aiki, suka kira yanjarida domin gewaya don suganema idanunsu wannan matsala domin isarwa Gwamnati da rokonsu da kuma Dan abundn suka iya aiwatarwa a matakinsu.
Da suke zantawa da manema labarai, bayan wannan kewaye, Alh Zahraddeen Sani Zakka Mal. Abdulakdir Ango Saulawa sun zayyana irin tashin hankali da rashin tabbas da wadannan al'umma suke cikin a shekara da shekara sakamakon rashin wadatattun hanyoyin ruwa, Wanda kamar yadda sukace, hakane yasa wasu dayawa suka kauracema unguwannin.
Dr. Muhammad Husamatu Abbas shima ya jaddada muhimmancin Samar da wadannan hanyoyin ruwa a wannan yanki, Wanda a ra'ayinsa, hakan zai baunkasa walwala da jindadi da tattalin arziki mazauna wannan wurare dama gari baki daya, kasancewar wannan hanya itace hanyar Sabuwar kasuwar Yar'kutungu dake cikin garin Katsina.
Dukkaninsu sunyi addu'ar samun Karin zaman lafiya da kwanciyar hankali da yalwar arziki a jihar Katsina dama kasa baki daya tareda kara jaddada rokonsu ga Gwamnati mal Dikko Radda kan ta sama musu wadatattun hanyoyin ruwa a unguwanninsu.