MUNA ZAUNE CIKIN YANAYIN BAN TAUSAYI- Mazauna Unguwar Sabuwar Low cost Dutsen Safe.
- Katsina City News
- 08 Jun, 2024
- 516
An bayyana Mazauna unguwannin Malali da sabuwar Low-cost a matsayin wadanda ke zaune cikin damuwa musamman a lokutan Damina.
Dakta Muhammad Husamatu Abbas mazaunin Unguwar Malali ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da yanjarida Jim kadan bayan zagayawa dasu don ganema idonsu irin matsalar fadadar hanyoyin ruwa da al'ummar wannan unguwanni suke Fuskanta.
Yace wannan matsala ta rashin hanyoyin ruwa tana barazana matuka ga kasuwancin al'ummar Katsina, musamman wannan hanya tana kaiwa ga kasuwar Yar' Kutungu da wasu makarantun cikin gari.
Dakta Muhammad Abbas yace mazauna wadannan unguwanni sun amsa kiran da gwamnati keyi na aiwatar da dai-daikun ayyuka a matakin unguwanni, amma wannan matsala tafi karfinsu, saboda haka, suke roko ga Gwamantin jihar kastina, da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki wajen kula da muhalli dasu kawo dauki na gaggawa a agaresu
Ya kara da cewa, wannan aiki yana bukatar kulawa ta gaggawa duba da yadda gidaje keta rugujewa sakamakon lalacewar wannan unguwanni, yana mai cewa al'ummar wannan unguwanni suna cikin yanayi na ban tausayi.
Mal. Muhammad Husamatu Abbas yayi roko ga maigirma gwamna jihar Katsna, mal Dikko umar Radda daya ziyarci wannan Unguwanni dakansa domin ganema idonsa yadda Girman wannan matsala take domin share musu hawayensu.
Unguwannin Bayan gidan taki da sabuwar low cost da Malali cike suke da dubban al'ummomi saidai babbar matsala mazauna wannan unguwanni itace rashin wadatatattun hanyoyin ruwa wadda take jaza rugujewar gidaje da asarar dukiyoyi a kowace shekara, musamman da damina.