Gwamna Radda na jihar Katsina ya bada umarnin kwace duk wasu gonaki ko Dazuka da aka bada ba bisa ka'ida ba.
- Katsina City News
- 01 Jun, 2024
- 409
Gwamnan jihar Katsina ya ba da umarnin kwace filayen dajin da aka bada ba bisa ka'ida ba
A wani mataki na kare yankuna da dazuzzuka masu muhimmanci, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., ya amince da rahoton wani kwamitin bincike da ya gano rabon filayen ba bisa ka'ida ba a matsayin filayen noma. Bayan amincewa, an fitar da wata wata takarda, kuma an kafa kwamitin da zai aiwatar da shawarwarin.
Gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakai don magance wannan matsalar:
1. An umurci mutanen da suka mallaki daji ko gonaki ba bisa ka'ida ba da su gaggauta ficewa daga wadannan yankuna.
2. Ana tunatar da jama’a cewa Gwamna ne kawai ke da ikon amincewa da rabon dazuzzuka da filayen gwamnati a garuruwan jihar Katsina.
3. An yi kira ga ‘yan kasa da su bi wadannan ka’idoji don gujewa illar da doka ta tanada.
Wannan sanarwar ta jaddada kudirin gwamnati na kiyaye ka'idojin muhalli da tabbatar da amfani da filaye yadda ya kamata.