AKAN SAMUN MATSAYIN DAKTA KO FARFESA ga abinda Prof. Abdallah Uba Adamu ya rubuta:

top-news


Da na samu D.Phil a 1988, na dinga liƙa ‘doctor’ a suna na, domin an fa na iso gari. Ba a yi shekara sai na haɗu da wani dogarin Sarki wanda ya dinga bayanai akan Ajami wanda ba ma taba tunani a kai ba. Nan da nan na daina liƙa ‘Dr’ ɗin a suna na. Sannan sai ga kuma ƙissar Annabi Musa da Halliru a cikin Surat Kahf, wanda ya nuna muhimmancin tawari’u ga Musulmi. 

Da na samu ‘Farfesa’ a 1997, sai na sake liƙa matsayin a sunanna – watau na manta ke nan da darasin farko na 1988! Nan ma na haɗu da mutanen gari waɗanda suka shanye ni a ilmin da ban ma taɓa kai tunani ba. Nan da nan na soke matsayin. Tun daga lokacin da na farga na daina maƙala ‘Professor’ a suna na.

Doctor ko Professor ba su ne ilimi ba. Su na nuna kawai ƙwarewa wajen gwanintar bin ƙa’aidar bincike. Wannan shi ne ‘philosophy’ ɗin. Sai a ce to ka ɗauki wani maudu’i ka gwada gwanintar ka a bincike. In ka yi nasara, sai a rattaba maka matsayin – amma ba wai ka fito a matsayin ‘masani’ ba ne. 

Duk waɗanda suka horar da ni tun daga ABU Turawane – Jack Reed, John May, Mike Burrage, Erica Glynn, Barry Cooper da kuma wanda ya fi Kowanne ɗorani a k an tafarkin bincike, Keith Lewin. Ba wanda nake kira ‘doctor’ ko ‘professor’, kai ko ma ‘Sir’. Hasali ma ba sa so a kira su haka – sai dai gundarin sunayen su na yanka kawai. 

Wataƙila aƙidar su ta bambanta da tamu ta girmama matsayi da malanta. Amma gara mu sani, zama doctor ko farfesa shi ne ma matakin farko na na neman ilimin gaske.

Wannan rubutun anyi shi kimanin shekara guda da wani abu da suka gabata 

NNPC Advert