Jam'iyyar PDP a Karamar hukumar Katsina Ta Gabatar da Shugabanninta na Riƙo da Dantakarar Ciyaman
- Katsina City News
- 26 May, 2024
- 548
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Lahadi 26 ga watan Mayu ne jam'iyyar PDP ta jihar Katsina ta gabatar da sabon shugaban jam'iyyar na riko a karamar hukumar Katsina tare da mataimakansa, a cikin shirye-shiryen zaben kananan hukumomi dake karatowa.
Alhaji Ibrahim Galadima shine sabon shugaban jam'iyyar ta PDP a matakin karamar hukuma wanda ya amshi takardar amincewa daga uwar jam'iyya ta jihar Katsina bisa wakilcin Mataimakin Shugaban jam'iyyar PDP na jiha, Hon. Ibrahim Magaji Danɓachi.
Haka kuma Jam'iyar a PDP ta gabatar da Hon. Yasir Ibrahim a matsayin wanda zaiyi Takarar Shugaban karamar hukumar Katsina a zaben 2025 na kananan hukumomi.
Taron da aka gudanar a babban Ofishin Jam'iyyar PDP na jihar Katsina dake kan titin kano ya samu halartar manyan 'Ya'yan Jam'iyyar PDP da wadanda suka taba takara a matakai daban-daban. Tsohon Danmajalisar karamar hukumar Katsina a matakin tarayya Hon. Aminu Ahamed Chindo, Alhaji Hamisu Maraya, Hon. 'Yantaba na daga cikin Mahalarta taron.
A wajen Taron Hon. Aminu Ahamed Chindo ya ya bayyana matsayarsa a jam'iyyar PDP tare da irin yanda ya samarwa fiye da mutum 115 Aiki a cikin kwanakin da basu fi watanni tara da yayi a lokacin da yake a matsayin Danmajalisar wakilan tarayya kafin a kwace masa.
Shima a nasa jawabin sabon shugaban riko na jam'iyyar PDP a karamar hukumar Katsina ya bayyana jin dadin sa yanda 'ya'yan Jam'iyyar ta PDP suke kara samun hadin kai da goyon baya,yace wannan yana kara masu kwarin gwiwa a Nasarar zabe na kananan hukumomi da za a gudanar a shekara 2025.
Haka Jam'iyyar ta PDP ta bude Ofishin Jam'iyyar a karamar hukumar Katsina dake kan titin barhim a cikin birnin Katsina.