"Gwamna Radda ba Marowaci bane, kuma baya tare da Marowata" Bala Abu Musawa ga Zababbun 'Yan Takarar Karamar Hukuma.
- Katsina City News
- 23 May, 2024
- 485
Alhaji Bala Abu Musawa Mataimakin Shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina, ya bayyana haka a zagayen da suke kakanan hukumomi 34 na jihar Katsina don neman hadin kan 'ya'yan jam'iyyar APC bayan zaben fidda gwani na 'Yan takarar kujerin kananan hukumomi da za gudanar a Katsina shakara mai kamawa.
Musawa ya isar da sakon Gwamnan Katsina a kan cewa dukkanin shugabannin jam'iyyar APC na kananan hukumomi su shiga lungu da sako na kananan hukumomin su don jawo wadanda suke ganin an masu ba daidai ba, don a fahimci juna.
Kwamitin a karkashin jagoranci Babban mai bawa gwamnan jihar Katsina shawara akan harkokin siyasa Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo, tare da Uwar Jam'iyyar APC ta jihar Katsina bisa wakilcin Mataimakin Shugaban jam'iyyar na jihar Katsina Bala Abu Musawa, suna zagayawa jihar Katsina da kananan hukumomi 34 don neman hadin kan 'ya'yan jam'iyyar bayan tsogunguma nan da can da suka biyo bayan zaben fitar da gwani na takarar shugabacin karamar hukuma a jihar Katsina.
Zagayen ya fara da Yankin Daura a kananan hukumomin Daura, Mai'adua, Sandamu, Baure, Zango, Kankiya, Kusada, Mashi da Ingawa.