Majalisar Kano Zata Yi Gyara Kan Dokar Da Ta Rarraba Masarautar Kano Gida Biyar, Ta Kuma Tsige Sarki Sanusi
- Katsina City News
- 21 May, 2024
- 303
Majalisar dokokin jihar Kano, ta gabatar da kudirin dawo da kudirin dokar gyara masarautun jihar Kano.
Hakan dai ya biyo bayan zaman tattaunawa ne da kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya yi a zauren majalisar.
A wani kudiri na gaggawa ga jama’a da shugaban masu rinjaye Alhaji Lawan Hussaini Dala ya gabatar, ya bukaci majalisar ta goyi bayan kudirin don ciyar da jihar gaba.
Mamba mai wakiltar Dawakin Shu’aibu Rabi’u ne ya goyi bayan kudirin na muhimmancin jama’a.
Idan ba a manta ba, a shekarar 2019 ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa wasu masarautu guda hudu, waɗanda suka kawo adadin sarakunan masu daraja ta daya a jihar zuwa biyar.
A watan Satumba na 2020 majalisar ta zartar da kudurin dokar gyara masarautun na 2020 wanda ya tanadi cewa Sarkin Kano ya zama shugaban Majalisar Sarakunan, inda ya kawo karshen batun karba-karba a tsakanin masarautun biyar masu daraja iri guda.