Ta’addancin ’Yan Bindiga Ya Ragu Da Kashi 70 A Katsina - Dikko Radda

top-news


Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar rage ta’addancin ’yan bindiga da kashi 70 cikin ɗari a cikin shekara ɗaya da ta gabata.

Gwamnan ya ce an samu wannan nasara ne a sakamakon abin da ya kira kyakkyawan hadin kai tsakanin jami’an tsaro na sa-kai na jihar da kuma jami’an tsaro na kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa gwamnan ya faɗi hakan ne yayin wata hira da manema labarai a Yola babban birnin Jihar Adamawa, a yau Asabar.

Gwamnan wanda ya kai ziyarar aiki birnin Yola, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a samu ‘yan sandan jihohi da za a sanya su shiga yaƙin da ake yi da matsalar tsaro a ƙasar.

Gwamna Radda, wanda ya ce sun bullo da dabarar yakar barayin, ya kara bayani da cewa abin da ake gani yanzu ‘yan bindigar na kai hari ne a kauyuka da yankunan da suke surkuki, inda suke kona gidaje da kashe jama’a.