RASHIN TSARO: GWAMNA LAWAL YA YABA WA ƘOƘARIN JAMI'AN TSARO A KAN 'YAN BINDIGA, YA KUMA JAJANTA WA AL'UMMOMIN DA ABIN YA SHAFA
- Katsina City News
- 15 May, 2024
- 382
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya jinjna wa ƙoƙarin jami'an tsaro na haɗin gwiwa game da sabbin hare-hare da nasarorin da su ke samu a kan 'yan bindiga a jihar.
A ƙarshen makon da ya gabata, rundunar sojojin ƙasar nan ta aika da wasu ƙarin jami'an ta, a wani yunƙuri na sake fatattakar ayyukan 'yan bindiga a yankunan da abin ya yi ƙamari a jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau yau, ya bayyana dirar mikiyar da sojojin suka yi wa 'yan bindigar a matsayin mataki na dagula harkokin miyagun 'yan ta'addan a Zamfara.
Sanarwar ta Sulaiman Bala ta kuma jajanta wa al'ummomin da harin 'yan bindigar ya shafa a 'yan kwanakin nan, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar na nan tana ci gaba da baiwa jami'an tsaro cikakken haɗin kai don shawo kan lamarin.
Sanarwar ta ce: “Ayyukan yaƙin da sojoji ke gudanarwa a wuraren da rashin tsaro ya yi ƙamari a Zamfara, abin a yaba ne, musamman bisa la'akari da irin nasarorin da aka samu tun lokacin fara ƙaddamar da munanan hare-hare kan 'yan ta'addan a ƙarshen makon da ya gabata.
“Wannan aiki ya samu Gagarumar nasara a yankunan Ƙananan Hukumomin Bungudu, Tsafe, Maru, da Zurmi, wanda ta kai ma hallaka wani ƙasurgumin ɗan ta'adda, Abu Dan Dunkwuifa, wanda ya yi fice wajen addabar wasu ƙauyuka a Bungudu da Maru.
“A ƙauyen Magama Mai Rake ta yankin Dansadau da ke Ƙaramar Hukumar Maru, jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka gomomin 'yan ta'adda.
“Harin da sojoji suka sake kai wa a Nasarawan Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum ya yi sanadiyyar ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su a ƙauyukan Kamaru, Tungar Rogo, da Matsare, tare da ƙwato shanu da dama da aka sace.
“Jita-jitar cewa an yi garkuwa da mutane sama da 500 ƙarya ce ta wasu mutane da ba sa son zaman lafiya ya dawo Jihar Zamfara. Mafi akasarin yankunan da ke fama da rashin zaman lafiya a Zamfara na ci gaba da samun taimakon soji, inda ake samun sakamako mai kyau.
Gwamnan ya kuma jajanta wa al’ummar da ’yan bindiga suka kai wa hari a jihar.
“Gwamnatin jihar Zamfara na son nuna alhini ga al’ummomin da ’yan bindiga suka kai wa hari kwanan nan. Mun himmatu sosai wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.
"Gwamnatin mu za ta ci gaba da tallafawa sojojin da ke yaƙi da rashin tsaro tare da bayar da duk wani tallafin gaggawa ga waɗanda rikicin 'yan bindiga ya shafa a jihar."