Takaitaccen Tarihin Kofar Kwaya Dake Birnin Katsina

top-news

Daga Saliadeen Sicey 

Kofar Kwaya tarihi ya nuna cewa ta samo asali ne daga wani Basarake Bahaushe mai suna Sarkin Kwaya, wanda ke mulki a wani gari da ake kira Kwaya, da ke kudu da birnin jihar Katsina.

Aikin da yake yi wannan Basarake shi ne, sama wa Sarki hatsi, kamar irinsu su dawa da gero da sauransu, domin amfanin gidan Sarkin a wannan Zamani.

An ce, ta ita wannan Kofar Kwaya ce Wali Jodoma, wanda Sarkin Katsina na lokacin ya kora, ya bi ya fita ya bar Birnin katsina.

Tarihi ya nuna cewa, da shi wannan Waliyyin zai fita, sai ya juya da baya ya tsinewa kofar ya ce, “ba za a yi wani abin kirki a kofar ba, sai bayan karni guda.

Ga yadda Katsinawa ke cewa, kusan kowace kofa ta sami ci gaba Amma banda kofar kwaya.

To A Wannan Zamanin Da ta ke samun Ci Gaba Karnin Ne Ya Cika.

Ita wannan kofar, Ana kyautata zaton A karni na 15 ne aka gina ta.

Ita ce yanzun Za ka iya bi ka je Dutsinma, Runka, Kankara, Funtua Zariya, Kaduna, Abuja da Sauransu.

NNPC Advert