KADAN DAGA DALILAN DA SUKA SA TURAWA INGILA SUKA YAKI DAULAR USMANIYYA.
- Katsina City News
- 09 May, 2024
- 542
Acikin karni na 20 ne Kasashen Turawa suka mamaye Kasashen Afirika, da niyyar su mamaye kasuwannin su da Kuma samun maadanai dake cikin Kasashen Afirika. Manyan Kasashen Turawan da suka shigo Afirika a wancan lokacin sune Ingila, Faransa, Jamani, Italiya, Fotugal da sauransu.
Tun cikin karni na 19 Turawan mulkin Mallaka sun fara kulla huddar kasuwanci da manyan Kasashen Afirika, inda suka bude manyan Kamfanonin kamar ( Royal Niger Company) da sauransu. Lokacin da Clapperton ya ziyarci Daular Usmaniyya a lokacin, acikin karni na 19, ya nemi yarjeniyar Kasuwanci tsakanin Daular Sokoto da Kasar Ingila, Wanda har Sarkin Musulmi Muhammad Bello ( 1817-1835) ya sa hannun yarjeniyar Kasuwanci tsakanin shi da Clapperton.
Ta hakane Turawan Ingila suka samu damar kutsowa cikin Daular Usmaniyya, suna leken asirinta.
Acikin shekarar 1900 ne Turawan Ingila suka fara rubuto wasika zuwa ga Sarkin Musulmi Attahiru na I, da niyyar cewa Daular Sokoto ka koma karkashin ikon Ingila, Wanda shuwagabanin Daular suka ki amincewa da wannan. Acikin shekarar 1903 ne Turawan Ingila suka shigo Daular da niyyar Yaki, inda suka Yaki Daular Sokoto. Turawan mulkin Mallaka sunci Sokoto da Yaki acikin wannan shekarar (1903). Sannan suka bi sauran Garuruwan dake karkashin Daular daya bayan daya suna yakarsu. Misali sunci Kano da Yaki a lokacin Sarkin Kano Aliyu Babba acikin shekarar 1903. Hakanan sunci Katsina da Yaki alokacin Sarkin Katsina Abubakar acikin shekarar 1903. Da sauransu.
Babban dalilin zuwan Turawan mulkin Mallaka Daular shine don su tashin tattalin Arziki su Kuma mamaye manyan kasuwannin Daular don ci gaban Kasashensu. Baya ga wannan sun kawo addinin Kiristanci a wasu sassa a Daular bayan sun cita da Yaki. Misali Turawan Mishan ( Crisstian Missionaries) sun yada addinin Kiristanci acikin Daular harda Katsina.
Wasu Sarakunan Musulunci na Daular sun nuna rashin goyon bayan su ga Yunkurin Yan Mulkiin Mallaka, Wanda su Kuma suka dauki mataki akansu, a inda aka tube wasu daga Sarautarsu, aka tafi dasu aka tsare.
Acikin shekarar 1902 zuwa 1930 an tsare wasu daga cikin Sarakunan Daular Usmaniyya, a Lokoja, saboda tawaye da rashin biyayya da suka nuna ga Turawan mulkin Mallaka na Ingila.
Daga cikin Sarakunan da aka tsare akwai ;-.
1. Malam Muhammad Lawal Kwasau. Sarkin Zaria, an kamashi 1902 an kaishi Lokoja 1904 ya rasu a Lokoja 1918.
2. Sarkin Kano Aliyu Babba. An kamashi 1906. An kaishi Lokoja 1906. Ya rasu a Lokoja 1926
3. Ibrahim Nagwamatse. Sarkin Kontagora. An kamashi 1902. An kaishi Lokoja 1902. Yabar Lokoja 1903.
4. Malam Aliyu Dansidi. Sarkin Zaria. An kamashi 1921. An kaishi Lokoja 1922. Ya rasu a Lokoja 1926
5. Ibrahim Abuja. Sarkin Abuja. An kamashi 1902. An kaishi Lokoja 1902. Ya rasu a Lokoja 1902.
6. Malam Ummaru. Sarkin Bauchi. An kamashi 1902. An kaishi Lokoja 1902.
7. Malam Muhammad Sarkin Nasarawa shima an kaishi Lokoja, amma daga baya yabar Lokoja.
8. Sarkin Gumel Habu, shima an kaishi Lokoja, Kuma a Lokoja ya rasu.
9. Sarkin Katsina Malam Yero an kamashi a shekarar 1906. An kaishi Lokoja 1906. Ya rasu a Lokoja 1919.
Sources.
1. M. D. Suleiman. The Hausa In Lokoja(1860-1966)
2. Jounarl of Current RESEACH in African Studies.
Musa Gambo Kofar soro.