YUNKURUN MAHADIYYA A KATSINA WANDA YAYI SANADIYYAR CIRE SARAKUNAN DALLAZAWA DAGA MULKI.
- Katsina City News
- 08 May, 2024
- 619
Lokacin da Turawan Mullins Mallaka suka ci Daular Sokoto da Yaki acikin shekarar 1903 a Filin Giginya, Sai Sarkin Musulmi Attahiru na I, ya bada umarnin da ayi gudun Hijira zuwa Saudiyya, domin su ba zasu rayu a karkashin mulkin Turawa, wannan kiranne da Sarkin Musulmi yayi ya jawo da yawan mabiya Daular da sauran Sarakunan Wasu sassa sukayi tattaki daga Daular da niyyar tafiya Saudiyya, a hanyar sune suka tsaya a Burmi, a shekarar 1903, Wanda daga nannne Turawan mulkin Mallaka na Ingila suka zakaye su, aka sake gwabza wani sabon Yakin Wanda masana Tarihi suke Kira da ( Battle of Burmi) a wannan yakinne shi Sarkin Musulmi Attahiru na I, yayi shahada tareda sauran mabiya Daular Sokoto kusan su (200). Sannan Kuma Suma Turawan mulkin Mallaka sun rasa rayukansu, hadda shi kwamandan Sojojin Ingila, Mai suna Major Mash, anan ya mutu wajen Yakin Burmi a 1903.
Acikin shekarar 1906 Sai aka sake samun wani sabon Yunkuri Mai suna Yunkurin MAHADIYYA ( MAHADIYYA Movement). Wannan wani Yunkuri ne Wanda ke fada da mulkin Turawa. Yan MAHADIYYA sun rinka Kira suna nunama mutane cewa duk Wanda yabi mulkin Turawa ya kafirta, wannan Kira ya samu goyon bayan Malaman addinin musulunci da wasu Sarakunan Gargajiya.
A Katsina wannan Yunkurin ya samu goyon bayan wasu Malaman addini da Sarakunan Musulunci. Misali Hakimin Kogo da mutanen shi sunyi Hijira daga Kasar shi Faskari zuwa Tsafe, don nuna goyon bayansu ga Yan MAHADIYYA. Hakanan Kuma a Kasar Iya ( Iya District). an kashe Baturen Ingila. An babban tawaye da rashin biyayya ga mulkin Turawa a Kasar Pawwa.
Ta bangaren Sarakunan Katsina ( Dallazawa). Yunkurin MAHADIYYA a Daular Sokoto ya zama babban makami dake fada da mulkin Turawa da Kuma addinin Kirista. Rabe Gambo ya Fadi cewa Wanda ya assasala Daular DALLAZAWA a Katsina Malam Ummarun Dallaje mabiyin Darikar Qadiyyane, wadda Kuma itace babbar Darikar mabiya Daular Usmaniyya a wannan lokacin. Wannan yasa mafi yawan Sarakunan Dallazawa mabiya Darikar Qadiyyane. Lokacin da Yunkurin MAHADIYYA ya bullo a Daular Sokoto Sai suka samu goyon baya ga mabiya Darikar Qadiyya harda Katsina. Wannan dalile yasa Sarkin Katsina Abubakar da Yero suka Basu goyon baya. Danjuma Adamu, da Bashir Aliyu, da Usman Aliyu Kofar Soro sun bayyana cewa, lokacin da aka fara yakin Satiru a Sokoto , an Samo Yunkuri da tawaye a mafi yawan bangarorin Daular harda Katsina. Misali a Katsina, an Kai Hari a Barikin Sojojin Turawa, da wasu ofisoshin Yan mulkin Mallaka. Wannan goyon da Sarakunan Katsina suka bada Yana daya daga dalilan ciresu daga mulki. Misali an cire Abubakar a shekarar 1905 hakanan an cire Malam Yero a shekarar 1906.
Sources.
1. Al'dunmu jounal of Current RESEACH in African Studies. Reason for the Deposition of Traditional rulers by the British in Katsina Emirate. Dr. Bashir Sallau, Danjuma Adamu and Usman Aliyu Kofar soro.
2. The fall of Dallazawa Dynasty in Katsina Emirate. Malam Rabe Gambo
Musa Gambo Kofar soro