Matsalar Ruwan Sha; Al'ummar Ganye dake karamar hukumar Matazu sun shiga mawuyacin Hali
- Katsina City News
- 06 May, 2024
- 524
Matsalar Karancin Ruwan Sha Na Neman Kassara Rayuwar Al'ummar Unguwar Ganye Dake Yankin Mazoji "A" A Karamar hukumar Matazu- Babba Mazoji
Daga Abdullahi Muhammad Sheka
An bayyana mummunan yanayin karancin ruwan shan da a halin yanzu ke kokarin durkusar da dukkanin al'amuran yau da kullum. Mai yawan fashin baki kan harkokin siyasa da al'amuran yau da kullum da suka shafi talaka a kasa baki daya Hon Zaharaddeen Babba Mazoji ne ya bayyana haka ga taron manema labarai cikin makon nan.
Babba. Mazoji yace halin da al'ummar Garin Unguwar Ganye wadda ke cikin mazabar Mazoji "A" dake yankin Karamar hukumar Matazu a Jihar Katsina da cewa lamari ne mai matukar ban tausayi, ya kara da cewa yadda idonsa ya nuna masa irin halin da al'ummar Unguwar Ganye ke ciki lamari ne da ke tayar da hankalin duk wani mai kishin al'ummarsa. Yadda mata da ƙananan yara ke yin doguwar tafiya kafin samun ruwan da zasu kawo gida, lamari ne mai ban tausayi.
Dattijo Babba Mazoji ya kuma nuna hadarin dake tattare da tsintar kai acikin irin wannan mawuyacin halin da wadannan al'umma ke ciki, ci gaba da rayuwa a cikin irin wannan yanayi na iya kaiwa ga fadawa cikin annoba irin kwlara da sauran cututtuka masu saurin yaduwa.
Haka kuma yawaitar matsalar karancin ruwan sha na haifar da rashin zuwan yara makarantu da kuma harkokin tsaftace muhalli. Mazoji ya ci gaba da cewa halin karancin ruwan ya jefa daruruwan al'ummar dake rayuwa a wannan yankin, cikin tska mai wuya, inda ya bayyana cewa halin da ake ciki na neman Kassara harkokin karatu , lafiya da abubuwan da suka danganci bukatar ruwa. al'ummar wannan garu na cikin matsananciiyar bukatar dauƙin mahukunta domin magance wannan matsala
Zaharaddeen Babba Mazoji ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Jihar Katsina, kungiyoyin sa kai da sauran masu ruwa da tsaki dasu gaggauta kaiwa Al'ummar wannan yanki dauƙin gaggawa domin gaggauta magance matsalar baki daya, musamman samar masu da kungiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da sauran hanyoyin da zasu saukakawa al'ummar yankin.
A karshe Babba Mazoji ya bukaci Gwamnan Jihar Katsina Malam Umar Dikko Radda da sauran dukkan Masu ruwa da tsaki dasu gaggauta kaiwa Al'ummar Unguwar Ganye dauƙin gaggawa domin magance masu wannan matsala ta rashin ruwan sha wanda ke neman durkusar da harkokin yau da kullum na al'umma, musamman batun rashin isar yara makarantu sakamakon wahalar da suke sha kafin samo ruwan da za'ayi amfani dashi a gidajen su.
Daga shafin sky limit media