Zaben kananan hukumomi : Gwamnan Katsina baya da wani Dan takara
- Katsina City News
- 30 Apr, 2024
- 527
@ Katsina Times
Mai ba Gwamnan jihar Katsina shawara kan harkokin siyasa Alh Ya'u Umar Gwajo-Gwajo ya gargadi masu neman kujerun tsayawa takarar Shugabanin kananan hukumomi da kansiloli da su dena cewa Gwamnan jihar ne ya turo su dan tsayawa takara.
Gwajo-Gwajo yace sun samu rahotanni yadda wasu Yan takarar ke cewa Gwamnan jihar Malam Dikko Umar Radda ne ya basu damar tsayawa takarar.
Dan hakane Maiba Gwamnan shawara yace wannan ba gaskiya bane Gwamnan Ya bada dama ga duk Mai sha'awar tsayawa takara ya sai fom ya nemi Juma'a.
Gwajo-Gwajo yace Gwamnan jihar Malam Dikko Umar Radda mutum ne me mutunta demokaradiya dan haka kowanne dan jihar nada yancin tsayawa takara kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada madamar ya cika sharidan toka.
A don haka ne Mai ba Gwamnan shawara ke Jan hankalin Al'ummar jihar katsina dasu sani Gwamnan jihar bashi da Dantakara na kowacce karamar hukuma ko kansila