Najeriya ta zama abin dariya a tsakanin kasashen duniya - TY Danjuma
- Katsina City News
- 12 Apr, 2024
- 436
Tsohon babban hafsan tsaron Najeria, Janar Theophilus Danjuma ya bayyana matsalar tsaron da ta addabi kasar a matsayin abin kunyar da ya sanya Najeriya zama abin dariya a tsakanin kasashen duniya.
Danjuma ya bukaci gwamnatin kasar da ta tashi tsaye wajen daukar matakan da suka dace na dawo da kimar Najeriya da kuma tabbatar da tsaron jama'a.
Janar Danjuma yace 'yan kasashen waje ba za su yi sha'awar zuwa Najeriya ba domin zuba jari a cikin irin wannan yanayin da kasar ta samu kanta na rashin tsaro.
Tsohon ministan tsaron yace a halin da ake ciki yau, kasashen duniya na yiwa Najeriya dariya saboda gazawar da ta yi wajen samar da tsaro ga jama'ar ta.