ƁARAYIN DAJI SUN KWASHI MUTANE A YANKIN BATSARI
- Katsina City News
- 19 Apr, 2024
- 387
A daren jiya alhamis 18-04-2024, ɓarayin daji masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suka kai hari ƙauyen Zamfarawar Madogara dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina.
Ɓarayin sun kai samame a ƙauyen na Zamfarawa kuma sun kwashi jimillar mutane mata, maza da yara ƙanana har ashirin da takwas, 28, kamar yadda wani mazaunin garin ya bayyana ma wakilinmu, kuma sun kora su daji. Har ya zuwa haɗa rahotonnan ba'a ji ɗuriyarsu ba.
A wani labarin kuma ɓarayin sun kai hari ƙauyen Ƙasai wacce duk yanki ɗaya ne da Zamfarawa ƙauyen da suka saci mutane, inda suka cinna ma zabaron kara wuta,wanda yake yammacin garin na Ƙasai, kamar yadda majiyar ta tabbatar mana.