Hanyar 'Yan Tumaki Zuwa Danmusa ta zama Tsaka mai Wuya
- Katsina City News
- 18 Apr, 2024
- 385
Muhammad Aliyu, Katsina Times
Hanyar da aka bayyana a matsayin daya daga cikin hanyoyin mafiya hatsarin 'Yan bindiga a jihar Katsina itace tsakanin 'Yan Tumaki zuwa Karamar hukumar Danmusa.
Binciken da Katsina Times ta yi ya gano cewa babu ranar da 'yan bindiga basa kai samame a hanyar da rana ko da Daddare.
Wasu mazauna yankin sun shedawa Katsina Times cewa hakan yana da alaka da karancin jami'an tsaro tsoro da ke akwai a hanyar sabanin wasu hanyoyin da suke da cakin point mai yawa kuma hakan yasa matsalolin suka ragu.
An bayyana Tabarbarewa kasuwanci da razani da 'yan kasuwar suke ciki, musamman masu kawo kayan masarufi a kasuwar 'Yan Tumaki don mu'amula ta yau da kullum.
Rashin tsaro yasa kusan kowa ya kauracewa kasuwar dake ci duk mako, a dalilin haka yasa rayuwar mazauna yankin ta kara tsananta.
Ko a satin sallar karama da ta gabata saida barayin masu garkuwa da mutane suka budewa wata motar fasinja 'Yan yawon sallah wuta, duk da ba a samu a sarar rayuka ba, amma mutane sun jiji ciwo sun firgita saboda razani, ko da yake rahotanni basu bayyana an tafi da kowa ba a wannan ranar.