Mi ke faruwa a Kano: Wani Almajiri ya Fille Kan Yaro mai shekaru 10
- Katsina City News
- 11 Apr, 2024
- 558
MAI FARUWA TA FARU
Bayan kammala tattara bayanan farko...
Wannan Almajiri mai kimanin shekaru 20 a duniya yanke-take ya yanke wuyan wani yaro dan kimanin shekara 10 a duniya.
Almajirin da ya aikata wannan katobara yayin da ya kammala fille kan wannan yaro daga bisani ya jefa kan yaron da ya gille acikin masai.
Shi dai wannan matashin almajiri daman yana zuwa garin na kanwa ne domin karatun almajirta tareda malamin su, kasancewar sun dan saba da jamaa, amma rabon sa da garin na kanwa an haura kusan wata uku, yanzu kawai yazo garrin ne domin yin bikin sallah karama. Almajirin bai tsaya a iya fille kan yaron ba, daganan ya farke cikin yaron tare da fito da kayan cikinsa.
Wannan lamari yafaru ne a garin Kanwa na karamar hukumar Madobi dake nan jihar Kano.
Rahotanni sun ce tuni fusatttun matasa na wannan yankin sukai rajamu tareda kashe wannan Almajiri dayayi wannan aika-aikar har lahira.
Izuwa yanzu tuni aka tura jami'an tsaro zuwa yankin kuma sun dauke gawarwakin guda biyu zuwa caji ofis na garin Kwankwaso domin fadada bincike.
Aminu Bala Madobi 11 Aprilu 2024.