TATSUNIYA (6) Labarin Yarinya Kyakkyawa Da Wanta
- Katsina City News
- 09 Apr, 2024
- 592
Ga ta nan, ga ta nanku.
An yi wani mutum a wani dan kauye yana da mata da 'ya'ya. Ana nan, sai daya daga cikin matansa ta haifa masa yarinya kyakkyawa.
Bayan kwana bakwai sai ya rada mata suna Kwambal. Sannu a hankali, kwanci-tashi, yarinyar ta girma, kyanta ya kara bayyana, har ya kasance duk garin ba mai kyau kamar nata.
Da ta isa aure sai mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa neman aurenta, wancan ya zo-wancan yazo, amma sai ta ki, haka aka yi ta fama, amma babu wanda ya yi nasarar samunta.
Kwatsam sai wani yayanta, wanda suke 'yan turaka, mai suna Dawi ya ce zai aure ta. Da Kwambal ta ji niyyarsa, sai ta ki ta ce yaya za ta auri wanda suke ubansu daya da shi?
Shi ko Dawi da man ɗan baiwa ne. Wata rana sai ya dauke ta a kan rakumi suka tafi cikin wani kungurmin daji ihunka banza, inda babu mutane.
Ashe da man ya ja ta dajin ne domin ya nuna mata hatsabibancinsa ko ta ji tsoro ta aure shi. Da fari ya rikida, ya zama wani babban bakin maciji, mai gemu da jajayen idanu da 'yan kunne. Sai ya fasa kai, ya kura mata jajayen
Idanunsa masu kama da garwashi., ya ce ta yarda ya aure ta, ko kuma ya cinye ta. Ita ko da kafewa, sai ta kekasa kasa ta ki.
Da ya ga haka, sai ya zama wani dodo mai hakora gatso-gatso da farata masu tsawo da kaifi da kofatai a kafafunsa. Yana cikin wannan hali ya sake cewa ta yarda ta aure shi, ko kuma a bakin ranta. Ita kuma ta sake kafewa faufau, ta ki. Haka dai ya rinka rikida, yana fito mata a kamanni da halittu daban-daban masu ban tsoro don ta ji tsoro, amma ta ki yarda, har ya gaji.
Sai ya dube ta ya sanar mata da aniyarsa ta komawa gida ba tare da ita ba, watau zai bar ta a dokar dajin nan tun da ta ki yarda. Yana gama gaya mata haka, sai ya kwantar da rakuminsa, ya dare, ya karya akala, rakumi kuwa ya kama tafiya.
Da ta ga ya bar ta, sai ta gyara muryarta tattausa, mai dadin sauti da ratsa rai, ta kama waka tana cewa:
Dawi dan'uwana,
Dora ni a kan rakuminka."
Da ya ji wannan waka, sai ya mayar da waka yana cewa:
"Ki ce ni mijinki ne,
In dora ki a kan rakumi."
Sai ta mayar masa a cikin wannan baitin:
"Ba ni iya fada,
Kai dai ka dora ni a kan rakumi."
Duk da wakokin da suke yi, bai tsaya ba, ita kuwa ta rinka bin sa tana yi masa waka da magiya ko ya dauke ta ya kai ta gida, amma sai ya ki, ya yi tafiyarsa shi kadai.
Da ta gaji, sai ta zaunaa gindin wata bishiya tana kuka. Can sai wani dodo ya ɓullo. Tana ganin dodo ta razana, ta yunkura za ta tashi ta gudu. Da dodo ya ga haka sai ya bude bakinsa mai feshin wuta da hayaki ya ce da ita: "Idan kika gudu zan cinye ki yanzun nan.
Tana jin haka sai ta tsaya. Da dodo ya ga kyawunta sai ya ce mata:
"Idan kin amince kika aure ni, zan kai ki gidanku, amma idan kika ki zan
cinye ki."
Da ta ga ba mafita, sai ta yarda ya aure ta. Suka tafi gidan dodo, ta dangana, ta zauna da shi.
Suna nan, har dodo ya tambaye ta irin abincin
da takan ci, sai ta ce nama ta fi so. Duk yayin da ya fita farauta sai ya kaso namun daji ya kawo mata nama da yawa.
Duk dare 'ya'yan dodon sai su fara cewa suna jin warin mutum, kuma suna so su ci naman mutum. Ita tana can inda babansu ya boye ta. Da zarar ta ji irin wannan magana ta 'ya'yan dodo, sai ta wurga musu irin naman da ubansu ya kawo, sai su ɗauka su tafi. Kullum haka take fama da su.
A can gidan su Kwambal kuwa, bakin cikin duniya ya dami mahaifiyarta, kuma tuni ta shiga cigiyarta, har wata rana ta hadu da tattabara. Baicin sun gaisa da tattabara, sai ta tambaye ta ko ta ga 'yarta Kwambal?
Da tattabara ta ji wannan tambaya, sai ta kada fuffuke, ta dubi gyatumar Kwambal ta kada baki ta ce: "E, na gan ta ammna tana gidan dodo suna zaman aure.
Jin wannan labari ya kara tayar da hankalin uwar, nan take ta barke da kuka. Can dai ta daina kukan, ta share hawaye ta dubi tattabara ta ce da ita:
"Akwai kuwa yadda za a yi a kubutar da ita daga hannun dodo?
Tattabara ta ce: "E, akwai wata dabara. Tun da dodon yana da gashi, a aika wa Kwambal cewa ta gaya masa za ta yi masa kitso a gindin kuka.
A cikin kagara uwar Kwambal ta ce: "To daga nan fa? Sai tattabara ta ci gaba da bayani: "Idan ta yi kananan tsoraye sai.
nuna masa daga nan kuma sai ta debi gashinsa mai yawa ta daure shi da
shi a jikin kuka. Idan ta daure shi bajau, sai ta tashi ta kama hanyar gari da gudu."
Da uwar Kwambal ta ji wannan shawara sai ta ji dadi, ta yi wa tattabara alkawari idan 'yarta ta kubuta za ta ba ta tukuici mai yawa. Sai tattabara tashi sama ta kama hanya har gidan dodo, ta sauka a kan dakin Kwambal to
fara waƙa tana kiran sunan Kwambal tana cewa:
"Kin yi tagumi 'yar auta,
Ki daina kuka `yar autar iya,
Idan ya dawo 'yar auta,
Ki kai shi gindin kuka 'yar auta,
Ki yi masa kitso yar auta,
Ki kitsa kanana 'yar auta,
Ki nuna masa 'yar auta,
Ki debi mai yawa 'yar auta,
Ki daura a jikin bishiyar kuka 'yar auta,
In ya dauru ki kama hanyar gida."
Ta rinka maimaita waka har Kwambal ta fara jin waka sai ta fita. Ta saurari wakar tattabara da kyau sai ta fahimci bayanin tattabara. Washegari da dodo ya zo dakinta sai ta ce za ta yi masa kitso amma a gindin kuka, sai ya yarda ya fara jin dadi matarsa za ta yi masa kitso.
Suka tafi gindin bishiyar kuka ta fara yi masa kitso, idan ta kitsa dan siriri sai ta nuna masa
sai ya ji dadi, idan ta debi gashi mai yawa sai ta daura a jikin bishiya har ta gama yi masa kitso.
Da ta ga dadin kitso ya sa ya fara gyangyadi, sai ta yi sanda ta janye jikinta ta fara gudu ta kama hanyar gari. Da ya farka sai ya hangi matarsa na gudu, idan ya yunkura zai tashi sai ya ji kansa a daure a jikin bishiya. Ya yi ta birgima a gindin bishiyar yana kuka yana ta birgima. Iya kokarinsa don ya kubuce amma sai abu ya gagara. Ita kuwa Kwambal
tana ta sheka gudu ba ta tsaya ba har ta isa gida. Haka ta bar dodo a daure.
Kurungus.
Mun Ciro wannan labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman