Gidauniyar Kafin-soli/Doka Ta Ba Marayu Tallafin Kayan Sallah.
- Katsina City News
- 30 Mar, 2024
- 424
Daga Mohammmad A. Isa, Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Gidaniyar Tallafa wa Marayu, Marasa karfi da marasa Galihu, ta "Kafin-soli/Doka Community Charity Fondation(KDCC)" a Turance, ta Tallafawa Marayu da Marasa karfi da kayan Sallah.
Gidauniyar ta bayar da Tallafin ne kamar yadda ta saba yi duk shekara, a ranar Asabar din nan 30 ga Maris, 2024 a garin Kafin-soli da ke karamar hukumar Kankiyar jihar Katsina.
Tallafin wanda ya hada da Shaddodi, Turame/Atamfofi, Abayoyi da sauransu da wasu 'yan canji domin dinkin sallah, na zuwa karo na Shidda kamar yadda shugaban gidauniyar Alhaji Suleman Garba Kafin Soli ya bayyana a jawabin da ya gabatar wajen taron.
Sama da Marayu da Marasa karfi 204 ne suka amfani da Tallafin, wadanda suka fito daga lunguna da sakon garin Kafin-soli/Doka da wasu 6angarori na karamar hukumar ta Kankiya.
Bugu da kari, an kuma dauko wasu Mutane daga kungiyoyi daban-daban da suka hada: Kungiyar Motocin haya na NURTW, Rumfunan zabe da Maza6u daga jam'iyyun APC,PRP, PDP, Kungiyar masu hayar Babura, Masu aikin sa-kai(Vigilante), Kungiyar yankasuwa,, Kungiyar kanikawa, Kungiyar Yan biredi,Kungiyar Teloli, kungiyar Masu aikin Computer da sauransu, inda su ma suka samu nasu Tallafin kayan Sallahn.
Dayake jawabi a taron, shugaba gidauniya mai membobin mutane 25, Alhaji Sulaiman Kafin-soli ya bayyana yadda gidauniyar ta faro kusan shekaru 6 da suka gabata, da kuma muhimmin aikin da gidauniyar ta saka a gaba wato Tallafawa Marayu musamman a garin na Kafin-soli/Doka
Alhaji Sulamain ya kuma bayyana cewar, ban da wannan Tallafi, akwai kuma wani tallafin da suke ba wasu mutane daban-daban a lokacin Azumi da Sallah, wanda ake bin su daidaiku ana ba su don dai a samun saukin rayuwa.
Daga karshe, an kuma kaddamar da gidauniyar a hukumance, wanda Iyayen kasa na Kankiya, Kafin-soli da Doka suka sa mata albarka.
Wadanda sukai Jawabi, da Shaidi bayar da Tallafin, tare da kuma kaddamar da Gidauniyar sun hada da: Tsohon gwamnan Borno General Abdulmumini Aminu wanda ya samu wakilcin mai garin kafin-soli, Alhaji Bello Abubakar Bello, da Barista Murtala Aliyu Kankiya wanda ya samu wakilcin Dallatun Kankiya, Kasim Yaro Kankiya, da tsohon dan takarar Ciyaman na Kankiya a karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Yusuf Abubabar Kafin-soli.
Sauran sun hada da: Iyayen Kasa; Hakimin Kankiya, da Maigarin, Radda Alhaji Kabir Umar Radda, da Alhaji Yusuf Nuhu, Abdulazizi Hallidu Kafin-soli, da Shugaban Karamar hukamar Ilimi ta karamar Hukumar Kankiya, da Malamai, masu fada a ji, da sauran al'umma.