FADA YA BARKE A TSAKANIN DABAR "YAN TA ADDA BIYU A DAJIN FAWWA DAKE KANKARA.

top-news


Muazu Hassan 
@ katsina times. 
Fada ya barke tsakanin dabar wasu "yan ta adda biyu dake dajin fawwa a karamar hukumar kankara. 
Dabar guda biyu daya ta Wani Dan ta adda ne mai suna Nahi, Dayar kuma sunan shugaban ta yellow.
Wata Majiya tace mana gonar wake ce ta haifar da rikicin inda yaran Nahi suka shiga gonar yellow ta wake sukayi masa barna.
Wannan dalili ya jawo  yellow da yaran su suka tunkari Nahi don daukar fansa.
Majiyarmu tace,anyi bata kashin da kowane bangare ya rasa yaran shi.
Wata Majiyar ma tace dukkanin shugabannin yan ta addar Nahi da kuma yellow an kashe su a wajen fadan.
Wannan lamari mai faranta rai ya faru ne laraba 31 ga watan agusta 2023.
Katsina times 
Www.katsinatimes.com 
Jaridar taskar labarai 
@ www.jaridartaskarlabarai 
07043777779 08057777762

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *