BABBAN BANKIN NAJERIYA (CBN) YA BIYA KUƊAƊEN DA AKE BI NA HADA-HADAR MUSAYAR KUƊAƊEN ƘASASHEN WAJE
- Katsina City News
- 21 Mar, 2024
- 482
Muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na bankin, Madam Hakama Sidi Ali, ita ce ta sanar da hakan ranar Laraba da daddare a Abuja. "gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya cika ƙudirinsa na warware bashin Dala Biliyan 7 da ake tuhuma".
Madam Sidi, ta ƙara da cewa yanzu haka babban bankin ya kammala biyan Dala Biliyan 1.5 domin warware matsalar kwastomomin banki, a matsayin biyan bashin abin da ya rage na hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje.
Ta kuma ƙara da cewa masu bincike na sa-kai daga (Deloitte Consulting) za su bibiyi wannan hada-hadar kuɗaɗen domin tabbatar da cewa iya waɗanda suka cancanta aka biya.
"Hada-hadar kuɗaɗen da aka yi ba bisa ƙa'ida ba za mu tura zuwa ga hukumomin da suka dace domin faɗaɗa bincike". Ya ƙara da cewa.
A wata ganawa ta kwanannan, gwamna Cardoso ya bayyana cewa "za mu ɗauki warware biyan duk wasu kuɗaɗe da ake bi kan hada-hadar musayar kuɗaɗen waje da muhimmanci domin dawo da martabar tattalin arziƙin Najeriya". Ya ce.
"Zan iya tabbatar muku cewa a yanzu dai mun warware sahihai, ingantattun matsaloli mun biya duk wasu kuɗaɗe na haƙiƙa da aka tura".
Biyan kuɗaɗen da ake bi kan hada-hadar kuɗaɗen da aka tura na ƙasashen waje ɓangare ne na wani shiri da aka yi a watan jiya domin daƙile tashin Dala da hauhawar farashin kayayyaki da samar da ƙarfin gwiwa ga bankuna da tattalin arziƙi.
CBN ta kuma bayyana cewa bayan hakan asusun ajiya na Najeriya a waje ya ƙaru daga Dala Miliyan 993 zuwa Dala Miliyan 34.11 a ranar 7 ga Maris, 2024 wanda hakan shi ne ƙari na ƙololuwa da aka samu a watanni takwas.