SHUGABA TINUBU YA DAKATAR DA BALAGURON JAMI'AN GWAMNATI ZUWA KASASHEN WAJE
- Katsina City News
- 21 Mar, 2024
- 365
Shugaba Bola Tinubu ya haramta wa ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje a aljihun gwamnati
Haramcin wanda zai dauki tsawon watanni uku a matakin farko zai fara aiki a ranar 1 ga watan Afrilu, 2024.
Haramcin ya zo ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Hon.Femi Gbajabiamila da sakataren gwamnatin tarayya George Akume wadda aka sanya wa hannu a ranar 12 ga watan Maris din 2024.
Wasikar haramcin ta kara da cewa, “Shugaban kasa ya damu da almabazzarancin da ke kunshe da tafiye-tafiyen jami’ai da sauran hukumomin gwamnati, da kuma bukatar da ke akwai ta mambobin majalisar ministoci da shugabannin MDA na su mai da hankali kan ayyukansu na cikin gida maimakon balaguro"
Wasikar ta ce “Bisa la’akari da kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu da kuma bukatar gudanar da harkokin kasafin kudi, na rubuto ne domin in isar da umarnin shugaban kasa na sanya dokar hana fita na wucin gadi ga dukkan jami’an gwamnatin tarayya a dukkan matakai har na tsawon watanni uku daga Afrilu 2024."
A cewar wasikar, "Wannan matakin na wucin gadi na da nufin tsuke bakin aljihun gwamnati a harkokin mulki don zuba kudin a bangaren gudanar da aiyuka ba tare da an an sami tangarda a tsarin gwamnati ba."
Tinubu ya kara da cewa, daga yanzu jami’an gwamnati da ke da niyyar tafiya duk wata ziyarar aiki a kasashen waje dole ne su nemi amincewar shugaban kasa a kalla makonni biyu kafin su fara shirin tafiyar, kuma fadar shugaban za ta amince ne da tafiyar kawai idan ta zama dole.
Idan ba a manta ba, a watan Janairu ne shugaba Tinubu ya ba da umarnin rage yawan tawagar masu yi masa rakiya da na mataimakinsa a tafiye-tafiyen cikin gida zuwa 25 da kasashen waje zuwa mutum 20 kacal.