Da Ɗumi-Ɗuminsu Rundunar Jami'an Tsaro Sun Aike Da Kachalla Damina Barzahu Tare Da Dama Daga Cikin Yaran Shi
- Katsina City News
- 19 Mar, 2024
- 714
Ƙasurgumin ɗan ta'addar nan da ya addabi jihohin Katsina da Zamfara, Kachalla Damina, ya gamu da ajalin shi tare da wasu daga cikin manyan yaran shi a wani artabun da aka gabza.
Biyo bayan bayanan sirri da aka samu Jami'an sojin Saman Najeriya sunyi dirar mikiya akan ɓarayin yayinda suke yunƙurin zuwa ƙauyen ƙwana dake cikin ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara March 10, 2024.
Damina, dai dama yana fama da jinyar wasu munana raunikan da ya samu yayin wata fafatawa da Jami'an, rundunar Operation Hadarin Dajia a yankin Dansadau, wanda yayi sanadiyyar da dama daga cikin ɓarayin dajin kan Babura.
Bayanan sirri sun bayyana ma Zagazola Makama, cewa kimanin babura 58 ɗauke da ƴan ta'addar yayin da suke yunƙurin kai hari suka sha ruwan wuta, ana kyautata zaton waɗanda suka tsira basu wuce Goma Sha Ɗaya 11 ba, Sama ƴan ta'addar Hamsin ne aka halaka su tare da ƙone baburan su, majiyar ta ƙara da cewa Jami'an tsaro na ci gaba da farautar giggan ɓarayin dajin da zumma gamawa dasu.
An Bayyana cewa Damina haifafen ƙaramar hukumar Kankara ne kuma shine yake addabar jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto da Katsina, Damina yayi ƙaurin suna wajen rashin tausayi da kisan wulaƙanci, a wani harin ma an bayyana cewa ya taɓa cire Jariri daga cikin Mahaifiyar shi ya kuma kashe su.
Rashin imanin Damina ya kai ga idan ya kama Mutane idan ya bayyana kuɗin fansar da yake buƙata matsawar ba'a kawo ba zai kashe waɗanda yayi garkuwa dasu.
Babbar maboyar Damina dai tana dajin Magami wani wuri da akafi sani da Kango ƙarƙashin jagorancin Buharin Daji da Nagala.
Wannan kisan da akayi ma Damina ya raunata daba dabar ɓarayin dajin wanda yanzu haka da damar su suke gudun tsira da rayukan su.
Damina ya samu horo ne wajen manyan ɓarayin daji irin su Shehu Rekep, da Alhaji Lawali Dumbulu, waɗanda sune suka fara harkar garkuwa da mutane a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto da Kebbi Inda maboyar su take a dajin Galadimawa Kuma ana zargin cewa suna samun makaman su ne daga ƙasashen Mali da Burkina Faso inda suke haƙar ma'adanai da kuma garkuwa da Mutane.