MAJIGIRI YA BADA TALLAFIN KAYAN ABINCI DA KUƊI GA MUTANE SAMA DA DUBU GOMA A MASHI DA DUTSI
- Katsina City News
- 17 Mar, 2024
- 542
Da safiyar yau Lahadi, mai girma Zaɓaɓɓen Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Mashi da Dutsi Hon. Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas Katsina).
Ya yi rabon kayan abinci da kuɗaɗen cefane ga al'ummar shi na ƙananan hukumomin Mashi da Dutsi domin samun sauƙin gudanar da Azumi.
Hon. Majigiri ya yi rabon kayan abincin ne a garin Mashi, inda ya raba kayayyaki wanda suka haɗa da:
1. Buhunnan Shinkafa
2. Katin-Katin na Taliya
3. Katin-Katin na Macaroni
Ɗan majalisar ya bayyana cewa wannan rabon kayan da yayi ya raba su ne domin rage wa mutane raɗaɗin halin da ake ciki na wannan yanayi.
Inda ya ƙara da cewa yana kira ga dukkan wanda aka damƙawa amanar rabon wannan kaya su yi adalci ta hanyar bayar dasu kamar yadda aka tsara.
Rukunin mutanen da suka amfana da tallafin a dukkanin ƙananan hukumomin na Mashi da Dutsi sun haɗa da:
1. Ƴan siyasa daga kowace rumfa (232)a ƙalla mutum 30
2. Shuwagabanin Jam'iyya
3. Hakimmai
4. Masu Unguwanni
5. Limamai
6. Ƙungiyoyin addinai na Ɗariƙa da Izala
7. Magaddai
8. Da sauran al'umma daban-daban.
Al'ummar da suka amfana da tallafin sun nuna jin daɗin su da farincikin su game da wannan abun alkhairi wanda Ɗan majalisar ya yi masu.
An gudanar da taron lafiya an kammala lafiya.
MAJIGIRI MEDIA TEAM
17/03/2024.