An kama wani gardi ya yi shigar mata a dakin kwanan ɗalibai mata a Kano
- Katsina City News
- 15 Mar, 2024
- 422
Jami’an Hukumar tsaron Farar Hula, wanda aka fi sani da 'Civil Defence' a jihar Kano sun cafke wani mutum mai suna Muhammad Munzali daga Kaura Gidan Damo a karamar hukumar Shanono a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta NSCDC, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wata sanarwa a yau Juma’a.
Ya ce Jami’an hukumar ne suka cafke wanda ake zargin da misalin karfe 10 na dare a ranar Laraba a lokacin da yake kutsawa cikin dakin kwanan dalibai mata na jami’ar Skyline Nigeria, da ke kan titin Sardauna Crescent, Nassarawa GRA, jihar Kano.
"Wanda ake zargin ya sa kayan mata sai ya yi shigar burtu zuwa dakin kwanan ɗalibai. Bayan an cafke shi, an same shi da layoyi a jikinsa," in ji PRO din.
A cewar Abdullahi, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin kutsawa cikin dakin kwanan dalibai na jami’a mai zaman kan ta, inda daga nan sai a dauki mataki na gaba.